Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 2 | 1001M10
==Ashe A Sakkwato Aka Tashi Yin Dakin Kaba?==

Allah daya amma kuma gari bamban! Haka Hausawa suka ce. Kowane gari babba, ko kuma mafi yawa, ko kuma da yawa za ka rika jin wasu maganganu wadanda sai ka rasa tushensu. Wasu labarai da jinsu, idan kana da hankali, ka san labarai ne na kanzon kurege, ko kuma labarai ne na kunne ya girmi kaka.

To a gaskiya wani labari da aka yi ta fadi a can baya game da Sakkwato, abin ya wuce kanzon kurege, ya ma wuce tuwon kurege idan akwai shi. Kuma labarin ya wuce labarin kunne ya girmi kaka, labarin ya zama labarin kunne ya girmi kowa.

Wannan labari mai ban mamaki ko ban dariya shi ne, wai a can dauri, a Sakkwato ne aka yi niyar yin Dakin Kaba, kuma a daidai inda masallacin Shehu yake a yanzu, to amma saboda rashin sa’a, ko kuma bisa kaddara, ana cikin salla a wannan masallacin na Shehu, sai wata karuwa ta gitta kuma tana jaye da bakin kare. Wannan mugun abu da wannan karuwa ta yi, sai aka fasa yin Dakin Kaba a Sakkwato aka mayar da shi a Makka!Abin Dubawa:

Duk da yake labarin ba gaskiya ba ne, babu ko kanshin gaskiya a cikinsa, amma manazarta al’ada da masu adabi za su iya tsintar wani abu, ko abubuwa masu amfani a nazarce, kamar:

a. Girman Sakkwato

Labarin yana nuna matsayin Sakkwato a idon wadanda suka kirkiri labarin, da kuma girmanta a idon wadanda ake bai wa shi. Babu wani wuri mai tsarki da girma a idon Bahaushe kamar Makka, ita kuma Makka ta sami wannan girma ne dalilin wannan daki, Kuma Sakkwato ta cancanci samun wannan daki baicin da wannan karuwa mai kare ta kawo matsala,

b. Girman Masallacin Shehu.

Masallacin Shehu har yanzu da gaske ne ya fi kowane masallaci matsayi a Sakkwato. Matsayinsa ya kara fitowa a wannan labari, inda aka nuna daidai inda yake aka tashi yin Dakin Kaba. Wannan ya nuna wannan masallaci ba karamin daraja gare shi ba, tun da har inda yake ya cancanci zama mahallin dakin Allah.

c. Girman Zunubin Karuwanci

Wannan labari, har yanzu yana nuna mana irin girman zunubin karuwa a idon wannan labari. Idan ka lura, wannan karuwa da aka ce ta yi sanadiyar dauki dakin Kaba zuwa wani waje, ba fa zaunawa ta yi ba, wucewa ne kawai ta yi, amma zunubinta ya haddasa irin wannan hasara ga wannan gari na Sakkwato.

d. Samakin Bakin Kare.

Har Yanzu wannan labari yana nuna cewa, kare musamman baki, ba karamin bakin jini ke gare shi ba. Don bakin jininsa ya taimaka wurin dauke wannan daki. Kuma har a wannan lokaci, wasu Hausawa na kallon kare a matsayin na gaba a wajen bakin jini.

Wannan wani haske ne ga mai bukatar sanin yadda ake nazarin labari don fitar da sakwanninsa.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124