Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 1 | 1001M11
==Gaisuwa Da Barazanar Da Take Huskanta==

Rubutu mai adireshi 1002M18 kamar yana son a ce wani abu a kan gaisuwa.

To, mai wannan rubutu ya yi farin ciki idan har gudun yake yi gaisuwa ta mutu a cikin Hausawa. Ba ta mutuwa har abada.

Sai dai kam idan gudun canjawarta yake yi zuwa wata, to ya sami wuri ya zauna tun yanzu ya soma kuka, don lallai canjawa za ta yi ta koma irin ta Bature ko ta koma shinkafa da wake. Alamomi masu yawa suna gwadin haka. Ni shahidi ne; kuma ganau ne; kuma karbau ne ga aikatau:

Wata rana na yi wani bako, tsohon abokina ne, ya kira ni na je tarbo shi, yana ganina sai ya yi tsalle zai rungume ni a matsayin gaisuwa, Allah Ya agaje ni na kauce da sauri. Na ji dadin kaucewar, duk da yake shi bai ji dadin haka ba. Amma ya karbi uzurina da na gaya masa cewa "Mu a nan Sakkwato wannan wayewa ba ta kai haka ba".

Sannan game da rashin tsayawa a gayar da manya, wannan ma zai kau, amma ba duka ba, ina ganin nan da wasu 'yan shekaru sai mutum ya gamu da surukinsa a hanya, ya daga masa hannu ya ce masa "HOW ARE YOU"? Na tabbata surukin zai iya karba masa da cewa "FINE", kowa ya wuce zuwa harkarsa.

A sha'anin Turawa wadanda Hausawa za su zama nan gaba kadan, kowa shi kadai yake, babu uwa, babu uba, babu da, babu ma kowa! Kowa harkarsa ta sha masa kai. Don haka babu mai lokacin wani.

Bature na iya korar uwarsa daga gidansa, to ballanta ubansa, to ballanta ma dansa, ballanta kuma wani dan'uwa. Don haka don ka ga dan'uwa ya kawar da kai don kada ka gaishe shi, ko don kada ya gaishe ka, ka gode wa Allah da bai kai ka lokacin da idan ka gaishe shi ya yi kararka ya ce kana bata masa lokaci da gaisuwa ko yawan surutu ba. Shin wai ko ba kada labarin Turawan da suka yi karar zakara a kotu a kan yana damunsu da kuka?

Idan ba kada labari duba wannan:
labarai-48877773


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124