Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 1 | 1001M13
==Ma'anar Akida==

Rubutu mai lamba 1025M2 ya nemi a yi masa bayani kan ma'anar AIKIDA. Sai dai mai rubutun bai yi bayanin a wane fanni yake neman wannan ma'ana ba. Saboda kalma kan iya canja ma'ana daga wannan fanni zuwa wani, ko daga ainihin ma'anarta a harshen masu ita zuwa wata ma'ana da aka ba ta a fagen wani ilimi.

To amma duk da haka, na yi dan yi kokarin neman wannan ma'ana a kamus-kamus na Hausa manya wadanda ake da su, amma ban ga dayansu ya kawo wannan kalma ba, ballanta ma'anarta.

To amma na nemi ma'anarta a Ingilishi a intanet sai na ga tana da ma'anar (ideology) da kuma (belief). Kana iya nema kai ma ka gani, musamman a google.

To amma a matsayina na Bahaushe, zan iya bayar da ma'anarta kamar yadda na fahince ta da Hausata, kuma ga abin da na fahinta:

1. A Mutanen Gari
Idan ka ji Bahaushe yana magana da dan'uwansa ya ce "Audu dan akida ne", yana nufin yana da ka'ida da ra'ayi wanda da kyar a iya canja shi.

2. A Malaman Addini
Idan ka ji malaman addinin Musulunci na magana a kan AKIDA, to suna magana ne a kan abin da ya shafi tauhidi, shi kuwa tauhidi ya shafi sanin Allah dangane da abin da ke wajibi gare shi da wanda yake korarre daga gare shi da kuma wanda yake ja'izi. Haka tauhidi ya kunshi sanin Annabawa da abin da ya kamace su, da abin da ya shafi mala'iku, da littafan Allah, da lahira, da kaddara.

3. A Malaman Hausa
Idan ka ji malaman Hausa na Al'ada suna magana a kan AKIDA, suna nufin imanin Bahaushe game da wasu abubuwa da ya yarda da su, kamar tsafi, da camfi, da maita, da kandu, da sauransu.

Abin Kula
Idan ka kula, a bayani na (1), a mutanen gari ana iya cewa AKIDA na nufin ka'ida. A lamba (2 da ta 3), a ilimin addini da ilimin Hausa, akida na nufin imani.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124