Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 2 | 1001M14
==Ba Ni Zuwa Kai Lefe==

Kafin shiga bayanin dalilina na kin zuwa kai kayan lefe yana da kau a san tushen maganar, kuma ga ta:

A dazu ne muke zance da wani abokina kan zancen auren wani, kwatsam sai ya ce mani "Litinin za a kai kayan lefe". Na ce "Na sani". Sai ya karba da cewa "Wata kila da kai za a je kai su". Da karfi na karba masa da cewa "Ni kam Ba ni zuwa kai lefe"!

Dalilina:
Kafin sanin dalilina shi ma ya kamata a san wannan:

Masana al'ada sun kasa matakan rayuwar mutane zuwa gida uku, watau:

1. Aure
2. Haihuwa
3. Mutuwa

A cikin wadannan matakai, a kowace nahiya ta duniya, za ka sami akwai al'adu a kewaye da wadannan matakai. Idan kuma ka duba al'adun da kyau, za ka sami sun kasu gida uku:

1. Na mata zalla
2. Na maza zalla
3. Na kowa da kowa (Mata da maza)

Wadannan su ne matakan rayuwa, kuma haka ake jera su, amma ni don in ji dadin bayyana dalilina na kin zuwa kai lefe, zan juya su, in mayar da samanu kasansu a haka:

1. Mutuwa
A al'adun mutuwa, idan ka duba a cikin Hausawa, za ka ga mata ne ke kukan mutuwa, mata na iya taruwa da gangan sun dinga kuka don su shaidar da wasu cewa an yi mutuwa a gida. Maza ba su kuka don shaida wa wasu an yi mutuwa. Idan ka ga maza na kuka a kan mutuwa, to kuka ne na hakika. Amma mata ba haka suke yi ba, suna kuka na hakika, watau na zafin mutuwar, suna kuma yi don sanarwa ga wasu, ko kuma don taya wani bakin cikin mutuwar wani nasa. Wani karin magana na cewa, kukan mutuwa ma buki ne. Watau wanda ya taya kuka kai ma ka taya shi kuka, wanda bai yi maka ba, kada ka yi masa. Wannan al'ada ce ta mata a wannan mataki na mutuwa.

Su ma maza a nasu bangare game da wannan al'ada, suna da wasu al'adu da suke yi wadanda su ne kawai ke yi. Kamar neman likkafani, da tanadin rufe wanda ya rasu.

A wannan bangare na mutuwa, za ka sami inda mata da maza suka yi tarayyar amsar gaisuwa. Watau mata na yin nasu gungu a cikin gida suna karbar gaisuwa, a inda maza su kuma suke waje da nasu gungun suna karba.

2. Haihuwa
A al'adun haihuwa, akwai al'adu da suka safi mata kawai, kamar karbar haihuwa, da wankan jinjiri da kayan barka. Su kuma maza sun karbi sha'anin hidimar zanen suna da taronsa da kuma neman abin yankawa. Mata da maza sun yi tarayya wajen nuna murnarsu a wannan rana, sai dai akan bar mata su ci gaba da buki da safe har zuwa faduwar rana, a inda maza kan koma gefe.

3. Aure
A aure ma an raba, akwai inda mata suka karba, akwai kuma inda maza suka karba, sannan akwai inda aka yi tarayya. Inda mata suka karba a shekarun baya, sun hada kai kayan lefe, da daukar amarya. Su kuma maza suka jibinci neman mata daga iyayenta, da daurin aure da kuma wankin ango. An yi tarayya a wajen buki, inda da safe akan yi murna, a bar mata su ci gaba da buki har zuwa faduwar rana.

Ni abin da na sani a garinmu, ban san yanayin naku ba. Kai kayan lefe da na barka na mata ne bisa rabon da kakanninmu suka yi. To ban san wanda ya tayar da wannan rabo ba, inda aka karbe wannan al'ada ta kai lefe daga mata aka bai wa maza. Kuma wai an ce har da maza ake zuwa daukar amarya, wanda wannan ma wani rabo ne na mata ake son kwacewa.

Ni har yanzu na rasa masu kirkiro wadannan al'adu ballanta in shiga neman masu juya su kamar haka. Sannan na rasa dalilin wannan canji da ake samu tsakanin wannan rabo da aka canja. Shin maza sun gano mata na kwaruwarsu ne wajen kai kayan lefe? Don an ce idan an kai kayan lefe a yanzu har da gurayen kaji kamar talatin zuwa sama duk ana iya dawo da su. Wasu sun ce wata rana har da gasasshen rago ake dawowa da shi. Idan haka ne to wayon a ci ne, wai an kori kare daga bakin dinya. Ko kuma a'a, su matan ne suka gaji da wannan wahala ta tattalar kayan lefe, suka yi wa maza wayo, suka bar masu ita? Idan haka ne kenan ana iya fassara wannan dabara ta mata ta cewa shigo-shigo ne ba zurfi. Babu mamaki su matan, son suke yi su ma su kwace wasu al'adu na maza, kamar neman aure, wata kila ma har da daurin auren.

Mai hankali bai kamata ya yi musun cewa mata za su daura aure a gaba ba, don ga shi maza dauke da kayan lefe a kawunansu, sannan su ne za su bi dare su dauko amarya.

Wannan a ganina babban canji ne aka samu a matakin rayuwa na aure, to amma ni a gaskiya wannan canji bai canja ni ba, don lallai kam (a yanzu dai) ba zan je kai kayan lefe ba, na kuma rantse!

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124