Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 1 | 1001M15
==Ashe Akwai Kabusu?==

Taba sigari, tana cikin abubuwan kyama ga Bahaushe, duk da yake daga samari har zuwa tsofaffi a cikin Hausawa kana samun masu shanta.

Taba ba ko'ina ake shanta ba, haka ba gaban kowa ake iya shanta ba. Kan wannan dalilin na kyama, da kyar a sami saurayin da zai sha taba bisa yardar iyayensa, sai dai ya sha ta bisa radin kansa.

Idan abu ya zama na kyama, Bahaushe yana da hanyoyin hana shi da yawa, kama daga bugu, zuwa fada, har zuwa kirkirar wasu labarai wadanda za su tsoratar daga aikata abin na kyama. Taba duka tana da wadannan matakai. A wannan rubutu zan duba wani labari ne da aka shirya watakila don tsoratarwa daga shan taba.

A lokacin da muke yara a nan Sakkwato, an sha ba mu labarin cewa "Kabusu shi ne wanda ya soma shan taba duk duniya"!

Kuma idan za a fada ana fadin wannan magana da karfin sauti, don nuna girman hadarin da ke cikinta. Kuma wannan Kabusu ana nuna mana cewa wani irin babban kafiri ne! Bisa ga al'adar Bahaushe yana kyamar abin da aka ce kafiri ne asalinsa, ko da kuwa shi kansa yana aikata shi.

Ina rike da wannan labari har zuwa girmana, har zuwa lokacin da na fara rarrabe wasu hanyoyin tsoratarwa na Bahaushe, inda na dauka wannan labari na Kabusu yana a cikinsu. A lokacin ma na dauka babu ma wani Kabusu da aka yi, illa kawai an kirkire shi ne don cimma wannan manufa ta tsoratarwa.

Haka nake har zuwa wajajen shekarar 2017, inda na sami wani wa'azi na wani malami mai ban dariya wanda ake kira Malam Mairahwani. Wannan wa'azi ya yi shi a garin Yawuri. Abin mamaki sai na je zancen wannan Kabusu a ciki. Ga dan abin da na tsakuro maku:

"....Ku bari a hwada ma kowa laihi ne, wanda ka tuba ya tuba, wanda bai tuba ya kara sabo. An yi su Hambalub Nu Kahakahatul Busadani! Da su Hukkakul Fattahul Bahili! Da Shalshabul Bahili! Da su Kabusab Na Dawudal Yahudi, wanda yah hwara shan taba. Dud duniya shi yah whara shan taba. Makiyin Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam. Duk suna ina"?....

Wannan shi ne zancen Malam Mairahwani da Sakkwatanci.

Idan an lura a ciki ya kawo zancen wannan Kabusu da nake magana. To amma kasancewar malamin ya cika wasa idan yana wa'azinsa, ban natsu da cewa akwai wadannan kafirai da ya zana ba, wadanda suka kunshi har da shi Kabusu. A takaice dai ban ma yarda akwai wani mutum mai irin wannan sunan ba, ballanta a yi zancen soma shan taba daga wurinsa.

To amma a yau na yarda da cewa akwai wani mutum mai irin wannan suna na (Kabusu), kuma wannan babban mutum ne don Sarkin Oman ne, Kuma mai karfin fada-a-aji a Gabas Ta Tsakiya. Sai dai akwai abin bakin ciki shi ne a yau ne wannan Kabusu shi ma ya rasu.

Karshe dai, a yau, na yarda da cewa akwai mai sunan Kabusu, amma abin da ban yarda da shi ba har yanzu shi ne, kasancewar soma shan taba sigari daga wani Kabusu. Babu mamaki a gaba in yarda idan na gano haka da kaina, ko kuma wani ya ganar da ni.

Mai son sanin halin kuma wannan Kabusu da na gano, ya duba wannan:

51073675


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124