Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 2 | 1001M16
==Kimiya Da Fasaha Da Ma'anar Kowane==

Tambaya mai lamba 1023M2, tana son ne a yi bayani kan ma'anar kimiya da fasaha. Tambayar kuma ta nemi a bayyana mata kalmomin da Hausa ta aro daga kimiya da fasaha, sannan kuma a rarrabe mata kalmomin, inda za a tsara kalmomin kimiya daban, na kuma fasaha daban.

Wannan tambaya kamar tana neman a yi mata wani littafi ne, wanda haka kuma ya fi karfin editan Makarantar Hausa. Abin da kawai zai ce shi ne:

Kimiya a Ingilishi tana nufin (science). Ita kuma fasaha a Ingilishi tana nufin (technology). (R. M. Newman,1997).

Ana iya bayanin (science), da cewa tsabagen nazari ne kan abubuwa na zahiri, da dabi'a. A binciki google da cewa (What is science).

Ita kuma kalmar (technology), tana nufin abubuwan da aka yi da wancan ilimi na (science). A binciki google da cewa (What is technology).

Zancen kalmomin kimiya da fasaha da mai tambaya ya nemi a tara masa, wannan ba zai yiyu ba ballanta a rarraba masu su. Abin da za a yi kawai, shi ne a aza shi bisa hanyar da zai yi wa kansa wannan jan aiki:

Akwai aikin M.H Jinju(1990). Wannan wani littafi ne da ya tara irin wadannan kalmomi.

Akwai aikin Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Ta Bayero (200?), mai suna Sababbin Kalmomi... Shi ma yana kunshe da irin wadannan kalmomi da kake nema.

Wadannan ayuka na sama, da yawa malaman su suka kirkiri wadannan kalmomi, ba wai Hausawa ne na cikin gari suka aro su ba, Amma malaman sun yarda a yi aiki da su.

Idan kana son wadanda Hausawa suka aro da kansu da kansu,

Ka sami Kamus na R.M Newman, 1997). Sai ka bi a hankali kana tsame su, tunda an gaya maka ma'anar kowane.

Abin Kula 1

Kalmomin kimiya wadanda Hausa ta aro ba su da yawa, saboda kalmomin da yawa sun shafi nazari ne mai zurfi, kuma idan kalmomi sun zama haka, da yawa sai ma'abuta wannan fanni kawai za su iya amfani da su. Ga kadan daga cikin wadanda aka aro a gefen kimiya:

1. netwok

2. intanet

3. sabis

4. asid

Abin Kula 2

Kalmomin fasaha su ke da yawa, don duk wani abu da aka yi ta amfani da ilimin kimiya, ko mutum bai iya amfani da shi, yana iya ganin abin, ko aikin abin da idonsa, ko ya ji shi da kunnensa. kamar:

1. mota

2. radiyo

3. talfo

4. kyamara

Da fata wannan zai zame wa mai tambaya jagora zuwa ga abin da yake nema.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124