Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 2 | 1001M17
==Mamakin Da Ke Cikinsu==
A yau aka cika kwana 22 a kan wata bukata da MH ta yi na cewa a duba wasu kalmomi guda shida don zakulo mamakin da ke cikin kowane. Wannan yana kunshe a wani rubutu mai lamba 1M108 da taken ==Ku Bambanta Su==. Kuma kalmomin su ne:

1. Karami
2. Kankane
3. Kankana
4. Kanana
5. Babba
6. Manya

Alhamdu lillahi, an sami wani mamba da ya ce wani abu a kansu a wani rubutu mai lamba 1009M22 kuma ya sami maki daga MH duk da yake bai yi abin da aka nema ba, amma duk da haka ya yi bajintar fitar da ma'anoninsu inda muka kara karuwa.

To, sai yau na sami damar farfasa mana wadannan kalmomi don zakulo mana dan abin da na gano game da mamakin da ke cikinsu. To amma kafin shiga fashin baki sai na canja masu tsari a haka:

1. kankane
2. karami
3. kanana
4. babba
5. manya

Idan an kula za a ga an cire (kankana), watau kalmomin a yanzu sun koma biyar kenan a maimakon shida. An cire (kankana) don sanin za ta fito a bayanin da za a yi:

To, wadannan dai kalmomi kowace sifa ce, watau (adjective) a Ingilishi. Kuma ita kalmar sifa tana sifanta wani abu ne da ke da wani abu, ko wanda bai da wani abu. Misali idan na ce (babba) ka fahinci wani abu wanda ke da girma. Idan kuma na ce (karami) ka fahinci wani abu wanda bai da girma.

Kalmar sifa a Hausa tana daukar nau'i uku:

a. Tilo namiji, kamar (kankane)
b. Tilo mace, kamar (kankanuwa)
c. Jam'i, kamar (kankana)

Duk wata kalma ta sifa da ta kasa samar da wadannan nau'uka, to ta zama abin mamaki. Ka gwada ka gani a matsayinka na Bahaushe, za ka idan dai kalma na sifanta wani abu, za ka ga tana da tilo na namiji da mace, haka tana jam'i. da kyar ka sami akasin haka, akasin kuma shi ne mamakin, mamakin kuma shi ne abin dubawa a nan:

1. kankane
Babu wani mamaki a kalmar (kankane) don tushenta (kankan) mun kara (e) mun sami (kankane); mun kara (uwa) mun sami (kankanuwa), mun kara (a), mun sami (kankana).

2. karami
To yanzu dauko mana lamba ta biyu watau (karami), tushe (karam). (i) muka kara muka sami (karami), za mu iya samun mace idan muka kara (a) watau (karama).

Ina jam'in karami? babu! Ba ka cewa (karumma), ko wani abu makamancin haka, sai dai ka ce (kanana) ko (kankana). Kenan abin mamaki a wannan kalma ta (karami), shi ne ba ta da jami'i daga tushenta. Da wuya ka sami irin wannan tsari a harshen Hausa, a ce ga kalma tana da namiji, kuma tana da mace amma bubu jam'i daga tushenta.
E! Yara kanana suna gyara wannan abin mamaki, idan suka ce karami; suka ce karama; sai su ce (karumma). Ni a gaskiya na fi ganin gaskiyar kananan yaran Hausawa bisa ga manyansu a wannan wuri, saboda manyan suna bin abin da suka ji ne kawai, alhali ya saba ka'idar kirar kalma ta Hausa wanda yara ke kokarin bi. Ku taya ni mamaki a wannan kalma!

3. kanana
Kalmar (kanana) ta fi kalmar (karami) ban mamaki, saboda ita jam'i ce kawai, babu tilo namiji ballanta tilo mace. Idan ka ce (kankane) shi ne tilon (kanana) ba ka yi daidai ba. Haka idan ka ce (kankanuwa) shi ne mace tilo na (kanana) ba ka yi daidai ba. Kankane da kankanuwa jam'insu (kankana) ba (kanana) ba. Kankana jam'i ne na karami ko karama. Wannan ma abin mamaki ne samun jam'in abu ba daga tushe daya ba.

4. babba
kalmomi uku da suka gabata watau (kankane da karami da kanana) duk suna nuni da abin da bai da girma. Ita kuwa kalmar (babba) tana nuni da abin da ke da girma. Kenan akasin na sama ce.

Mamakin kalmar (babba) shi ne, ba ta da mace ba ta da namiji, sannan uwa-uba ba ta da jam'i idan da tushenta za a yi. Namiji za ka ce (babba), mace za ka ce (babba), idan kuma za ka yi jam'i, sai ma ka bar kalmar gaba-daya ka dauko wata, ka ce (manya).
Wannan abin mamaki ne, don ba haka tsarin sifofin Hausa yake ba. Ko kalmar sifa ta zama mata-maza, za ka ga tana da jam'i daga tushenta, kamar kalmar (kurma), namiji da mace duka ana iya ce masu haka, amma idan za a yi jam'i sai a ce (kurame), watau an sami jam'i daga tushen kalmar ta (kurma).
Har yanzu yara kanana na kokarin gyara wannan abin mamaki, inda idan suka ce wa mace da namiji (babba), idan za su yi jam'i sai su ce (babbuna), watau su samar da jam'i daga tushen kalmar. Ina jinjina masu su yaran, duk da yake ina cike da mamakin wannan kalma.

5. manya
Mamakin wannan kalma ta (manya) ya bayyana a sama da aka duba mamakin kalmar (babba), don ita ce jam'inta. Wannan kalma, ba ta da namiji ba ta da mace daga tushenta. Babban mamaki ma ba ta ko kama, (ko a sautuka) da kalmar (babba) amma kuma an tilasta ta zama jam'inta.

Idan dai har an fahinci abin da aka duba game da wadannan kalmomi, to lallai za a ga cewa suna da abin mamakin da ya kamata a yi rubutu a kansa, kuma an yi din.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124