Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 1 | 1001M19
==Mutum-Mutumi Ne Daidai, Ni Ma A Ganina==

Mutum-mutumi da butum-butumi, kalmomi ne da ke yawo a matsayin abu daya, watau sifar mutum da aka kera da karfe ko da ice ko da roba ko da wani abu daban. (Kamusun Hausa: 2006)

Sai dai a ganin MH, akwai yiyuwar sojan gona ne daya yake yi wa daya kamar yadda wani mamba ya nuna a rubutunsa mai lamba 1009M43 a lokacin da yake karba wa MH. Wannan ya faru ne lokacin da ita MH ta bukaci yin nazarin wadannan kalmomi a rubutunta mai lamba 1M132

Idan mutum ya yanke hukunci, yana da kyau ya bayar da dalilinsa, ko da kuwa dalilin ba mai karbuwa ba ne a idon wasu. Ni ina ganin mutum-mutumi ne daidai, ba butum-butumi ba. Kuma ga dalilina:

Dalili Na 1

Idan muka ce mutum, ina ganin kowa ya san shi, watau kamar ni da kai. kalmar mutum takan rikida ta zama (mutumi). Kuma a Hausa ana iya linka kalma don rage mata karfi. Misali idan na ce (doki) ina iya cewa (doki-doki). Ina fadin haka, idan ina son in rage wa abu sifar doki. Kenan (doki-doki), abu ne mai kamar doki, amma bai cika doki ba.

Ta haka idan na ce (mutum-mutumi), ina iya nufin abu mai sifar mutum wanda bai cika mutum ba. Wannan ya yi dadai da fassarar kamus da aka bayar a sama, watau sifar mutum da aka yi da wani abu.

Idan ka cire linkawar da aka yi, watau ka ce (mutum) za ka sami cikakken mutum, idan ka linka, za ka sami mutum wanda bai cika ba.

Ita kalmar (butum), ita ma tana rikida ta zama (butumi), amma ba ta nufin mutum ko wani abu mai alaka da mutum. (A duba kamus na sama). Abin da take nufi (amya), watau tarkon zuma. To da wani dalili ne na hankali za a ce tana nufin wani abu mai kama da mutum? A dalili na hankali, butum-butumi, yana nufin wani abu mai kama da tarkon zuma, amma ba tarkon zuma ba ne na hakika, kamar yadda mutum-mutumi, ke nufin mutum, amma ba na hakika ba.

Dalili Na 2

Butumi da butum asalinsu karin harshen Zariya ne, su ke ce wa amya haka (tarkon zuma haka), Zariya kuma tana da makwaftaka da Katsina, kuma Katsinawa su ke cewa butum-butumi maimakon mutum-mutumi. (A duba Bargery, 1934).

Daga nan za mu iya lura da cewa, asalin butum-butumi daga Katsina yake, daga sannu-sannu ne, ya watsu. Ga alama kuma kuskure ne suka yi, saboda kalmomin suna da kama daya, da kuma halin rikida kamar daya.

Karshen Magana

Idan wasu sun yi kuskure, wasu sun karba, wannan abu ya zama karbabbe idan a harshe ne. Masu magana su ke da hakki a harshensu ba masu nazari ba. Don haka butum-butumi, ko MH ta yarda da shi ko ba ta yarda da shi, kalma ce ta Hausa. Abin da kawai wannan nazari ya yi shi ne lalaben asalin wannan kalma.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124