Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 2 | 1001M20
==E, Akwai (Q) A Hausa, Kuma A'a, Babu (Q) A Hausa==

Sharfaddeen ya yi tambaya, kuma ya sami amsa a rubutu mai lamba 1M129

A cikin wannan tambaya, shi Sharfaddeen, shi ya yi amfani da (q) a rubutunsa don neman bayani kan ka'idar rubuta Dasuki. Inda ya nemi a sanar da shi hanya daidaitacciya ta rubutawa. Dasuki za a rubuta ko Dasuqi?

Bayan wannan, wani mamba ya yi mamakin ganin (q) a cikin amsar da aka bayar, watakila ma har da ganinta a tamayar, har wannan abu ya sa shi tambaya da cewa "A Hausa akwai q"? A duba a nan 1M131M1023M1 a ga tambayarsa.

Abin da zance a nan shi ne, ana iya cewa akwai (q), kuma ana iya cewa babu (q). Amma a duba wannan don tabbatarwa:

==Akwai Q Hausa==
Rubutun Hausa na boko an sani cewa Turawa ne suka kirkire shi da kansu, suka kuma koya wa Hausawa shi, sabanin rubutun ajami da Hausawa suka kirkira da kansu. A lokacin da Turawa ke kokarin samar da bakake don wakiltar sautukan Hausa, sun sha wahala kafin a sami daidaita harufa masu lankwasa, ko harufa masu kugiya kamar yadda wasu ke kiransu. Wannan wuya sun sha ta ne kasancewar a Ingilishi babu irin wadannan sautuka. Wadannan sautuka su ne

b mai lankwasa
d mai lankwasa
k mai lankwasa

Bayan daidaitawa da yarda da a yi masu lankwasa, wata matsalar ta kunno kai bayan samuwar kwamfuta, saboda babu irin wadannan sautuka a kibod na kwamfuta, don haka aka yi ta dabaru don samar da wannan lankwasa a wadannan harufa. Daga cikin dabaru mafi shahara a yanzu a Najeriya, shi ne amfani da wani nau'in (font) wanda ake kira (Dr. Abdalla Uba Adamu). Ta amfani da wannan (font) za a iya samar da irin wadannan harufa masu lankwasa. Haka akwai wani (font) shi ma wanda ake kira (Rabiat Muhammad), shi ma wata dabara ce ta samar da wadannan harufa masu lankwasa. A wannan (font):

(v) tana zama (b) mai lankwasa
(x) tana zama (d) mai lankwasa
(q) tana zama (k) mai lankwasa

Duk wanda ya san da zaman wannan (font), ya san (q) ita ce (k) mai lankwasa. Sharfaddeen watakila ya sani, kuma MH ta sani. Watakila shi ya sa ya yi amfani da (q) a matsayin (k mai lankwasa), ita ma MH ta amsa masa ta amfani da (q) a matsayin (k mai lankwasa). Kuma ta yi haka ne bisa saninta da wannan (font).

Ka ga ta nan ana iya cewa akwai (q) a Hausa.

==Babu Q Hausa==
A sama mun ga dalili daya da zai iya sa a ce akwai q a Hausa, a yanzu kuma za mu duba dalili daya da zai iya sa a ce babu q Hausa.
Idan ana zancen harufan da aka aza don su wakilci sautukan Hausa, to babu q a ciki, ta nan za a ce babu q a Hausa.

==Wasu Dalilai==
Harafi ba shi ba ne sauti, sauti daban harafi daban. Harafi ba kome ba ne face wakili na sauti. Duk abin da aka ga dama aka aza yana iya zama wakili na sauti, wannan ya sa rubutun sautukan duniya suka bambanta. Don an ce q, ba shi ba ne hakikanin sautin k mai lankwasa. Don an rubuta k an yi mata lankwasa, ba ita ba ce hakikanin sautin k mai lankwasa, a'a wakilci ne kawai suke yi.

Idan haka ne, kenan duk lokacin da mutum ya matsu ya so rubuta k mai lankwasa, (kamar yadda watakila Sharfaddeen ya yi), amma ya kasa rubutawa, sai ya rubuta q, wannan ya zama wakili na abin da yake son fada, watau k mai lankwasa. Sako yake son isarwa a gane, kuma an gane. Don q ta wakilci sautin k mai lankwasa, kamar yadda ita kanta k mai lankwasa ba ita ba ce sautin ba, wakilci kawai take yi.

A nan kuma za mu ce, Idan hakikanin WAKILCI kawai ake nufi, to akwai q, idan kuma hakikanin WAKILI ake nufi, to babu q.

Abin nufi a nan shi ne, idan an yi amfani da wani harafi kamar q a matsayin wakilin sautin k mai lankwasa, akwai q, kamar dai yadda wasu ke amfani da (6), don ta yi wakilci ga sautin b mai lankwasa a lokacin da suka kasa samun damar rubuta b din mai lankwasa. A nan (6) ba (6) ba ce, (b) mai lankwasa ce.
Idan kuma an yi amfani da wani harafi a matsayin hakikanin wakili (harafin da aka yarda a rubuta Hausa da shi), kamar q, to an saba ka'idar rubutu, za a ce babu wannan wakili (harafi) a Hausa.

A nan ya kamata na tsaya. Watakila na dan zurfafa da bayani, babu mamaki wani abu ya shige wa wani duhu. Kada a damu, a tambayi abin da ba a gane ba.

Allah Ya taimake mu.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124