Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 1 | 1001M5
==Ma'anar Kai==

Ba wani kamus da na duba a halin yanzu game da ma'anar wannan kalma ta "kai". Kawai daga cikin kaina na ji su suna fita, shi ne na ce ban sani ba ko wani na da wani abu a kansa da zai kare ni game da wata ma'ana a kan wannan kalma ta "kai".

1. kai: Yana nufin abin da ke bisa wuya.

2. kai: Idan za ka kira mutum kamar "Kai Audu".

3. kai: Idan za ka aiki mutum ya kai wani abu.

4. kai: Yana nufin "isa", kamar "Audu ya kai gida".

5. kai: Yana nufin abokin magana, kamar "Kai nake son gani".

6. kai: Idan za a nuna mamaki, kamar "Kai! Wannan abu da girma yake".

7. kai: Yana nufin ainihin abu, kamar (Ni kaina, shi kansa).

8. kai: Yana nufin "sama", kamar "Abin da muke magana a kai", watau "Abin da muke magana a kansa".

Ma'ana ta (3) da (4), suna da dangantaka. Sai dai ta (3) aikatau ne so karbau, ta (4) kuma aikatau ne ki karabau.

Babu mamaki idan aka duba kamus a sami karin wasu ma'anonin.

Wani zai ga wannan ba kome ba ne, amma kuma wani abu ne a gun masu karatu ko nazarin ilimin Tsarin Sauti. Saboda wannan kalma ta "kai", haka ake rubuta ta, ba wani bambanci, tsayin wasali da karin sauti kawai ne ke bambanta ma'anarsu.

Wannan ta zame gudummawa ga daliban Tsarin Sauti.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124