Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 2 | 1001M6
==Gyara Kayanka==
Wani mamba mai lamba 1009 ya nemi a dan yi masa gyara ga wani muhimmin rubutu nasa mai lamba 1009M9

To ga dan gyaran da nake gani idan an yi shi abin zai kara inganta.

==1. Hargitsa Bayanai==
Bayani daya aka nema, watau bayanin TUKUDI, amma marubucin sai ya kawo bayanin wasu abubuwa da ba su da alaka da wannan abu da yake magana, watau TUKE da TARANAKI da TUKUKI. Bayanin da ya yi a kan wadannan sun amfanar da mu, sai dai ba su da alaka da babbar manufar bayaninsa. Ina ganin tukudi yana da alaka da fura da gumba, idan da bayanin wadannan abubuwa aka kawo tare da nasa da ya fi kyau ma.

Shawara a kan wannan ita ce a rarraba bayanan, kowane a yi shi da ban.

==2. Tukudi Da Tuke Da Tukuki Da Tarnaki Ba Saiwarsu Daya Ba.==
Marubucin ya nuna kamar wadannan kalmomi na sama saiwarsu daya, wata "TU" kamar yadda ya nuna, idan na fahinci yadda yake nufi a daidai, to lallai akwai 'yar mushkila ga bayaninsa. Saboda idan aka ce saiwar kalma a ilimin Kirar Kalma ana nufn sashen kalma wanda bai canjawa. Ta haka za mu ce saiwar tukudi ita ce "tukud" (babu wasali), don za a iya cewa (Tukudanta mani hatsin nan) idan ana son a mayar da hatsi tukudi. Ta haka za mu gane kowace kalma daga cikin wadannan kalmomi, saiwarta da ban take da ta 'yar'uwarta.

To amma wata kila yana son ne ya nuna gabarsu ta farko duka ta fara ne da "TU" idan haka yake nufi ya yi daidai, sai da kalmar TARNAKI ta farko, ta soma ne da "TA".

Marubucin yana iya duba yadda Makarantar Hausa ta gyara wannan rubutu nasa ta hannun editanta, kuma ta saka shi a shafinta na tambayoyi kuma yake da lama a can ta 1X2X7X2 .

Duk da haka ya kamata a girgiza wa mai wannan rubutu, don duk da gyaran da aka yi masa rubutun nasa ya sami karbuwa matuka a wajen Makarantar Hausa.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124