Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 1 | 1001M7
==A Nan Ma Akwai Abin Dubawa==

Ba mutane ba, ni kome ma a gare ni abin kallo ne. Kallo nake yi. Ka san don me? Ina kokari ne in gani ko na sami wani ilimi daga abin da nake kallo, ko a kan abin da nake kallo din.

Yara biyu ne a gabana, wasa suke yi, ba su san ina kallonsu da sauraronsu ba. Yara ne karami da babbba, amma duka ba su wace shekara biyar ba.

Babban haka kawai ya dauki yagiya ya daura wa marikin gambu (kyauren kofa), kuma ya dubi karamin ya ce masa "Sanuwa ce"! Shi kuma karamin ya zaburo ya rake yagiyar yana cewa "A sa mata mai"!

Haushi ya kama babban, sai ya bata huska, kuma ya aza dan yatsansa a kan goshin karamin, ya dangware shi yana cewa "sanuwa ake sa wa mai"?

Dariya ta kucce mani ganin irin wannan danyen hukunci. Shi babban bai kalli wautarsa ba, ta ce wa gambu saniya, amma ya ga wautar karamin da ya ce a sa wa saniya mai. Babban ya san babur ko mota ake saka wa mai don su yi tafiya, amma saniya ba a sa mata mai. Na yi mamaki kwarai da shi babban bai gano cewa ta yaya gambu zai zama saniya? Idan har gambu na zama saniya, to babu mamaki idan an sa wa saniya mai.

Abin dubawa a nan shi ne, kamar fa yadda yaran nan suka yi wannan wasan kwaikwayo, babu mamaki mu ma manya muna yin irinta, watau muna wauta a wajen wani bayani namu, amma ba za mu yi wa nakasanmu uzuri ba idan sun yi mana tasu wauta sakamakon wautarmu da muka yi masu.

A kan wannan nake gani, duk lokacin da muka ji wani ya yi mana wauta, kafin daukar kowane hukunci, ya kamata mu tambayi kanmu dalilin wannan wauta, idan ba mu ne sanadinta ba.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124