Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 2 | 1001M8
==Nok'awut A Bakin Masallaci==

Jiya ne da dare, na farka firgigit! Bayan natsuwa da na sama wa kaina, sai na gane nok'awut ne ake bugawa dalilin shigowar sabuwar shekara ta Miladiyya.

Kowane addini yana da abubuwan da yake girmamawa, wadanda babu mamaki su hada da wasu ranakun sati, ko wata, ko shekara, ko ma duk bayan wasu shekaru. To a addinin kirista daya ga sabuwar shekarar Miladiyya, rana ce mai muhimmanci a gare su. A ranar, suna yin wasu abubuwa da al'adunsu suka yarje masu, daga ciki akwai buga nok'awut da dare, kararsa da baltsin wuta da yake yi bai damunsu. Hasali ma wannan abin murna ne da farin ciki a gare su.

Ba ni mamaki ko kadan idan na ji karar bugun nok'awut a lokutan harkokin Kirista ko da kuwa a garuruwan Musulmi ne kamar Sakkwato, don kamar yadda ake iya samun Musulmi a ko'ina a Najeriya, haka ake iya samun Kirista a ko'ina a Najeriya. Mamakina kawai shi ne:

A al'adance Bahaushe yana da kyama sosai game da al'adun da ba nasa ba, yakan turza koyaushe ya ga bakuwar al'ada tana son shiga nasa, misali yadda ya tinkari waka a fanafinan Hausa, inda bai yi nasara ba. Kyamarsa da tsanarsa na karuwa su yi girma sosai a lokacin da ya huskanci al'ada daga wasu baki ne wadanda addininsa ya yi hannun riga da nasu. Misali kwallo, an shaida mana lokacin da muna yara cewa "An fara kwallo da kan jikan Annabi S.A.W". Na tabbata an yi haka ne don a cusa mana kyamarta. Amma a nan ma ba a yi nasara ba. To yanzu ga wata al'ada ta bullo ta bugun Nok'awut, kuma a lokacin harkokin da suka shafi addini, watau ganin watan Ramalana, da salla Karama hadi da salla Babba.

Dan Sakkwato ko mazauni Sakkwato ya san da wannan al'ada ta bugun wannan abu mai kara da baltsin wuta da firgitarwa, kuma abin mamaki an ce har a kofar fadar Sarkin Musulmi ana buga shi, kuma wannan fada tana gaf da masallaci na biyu a girma bayan Masallacin Shehu, watau Masallacin Bello.

Duk da yake an ce mazauna gari, an ce ma har da hukuma na son, ko kuma tana kalubalntar wannan abu, amma na tabbata ba za su yi nasara ba. Al'ada, al'ada ce, ba a iya taronta, idan ta bullo ta bullo ne, sai dai idan wadanda suka shigo da ita suka bukaci korarta.

Ka saurara mai karatu, a jiya ka ji bugun nok'awut na Kirista, A watan Azumi mai zuwa za ka ji bugun Nok'awut na Musulmi.

Ba na suka ko yabo a kan bugun nok'awut, haka ba na suka ko yabo kan masu buga shi, gurina daya ne, kuma shi ne in fito da yadda wata al'ada ta kunno kai, kuma ta kai har a bakin masallaci.

Wannan na tabbata, wata gudummawa ce ga manazarta al'ada.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124