Tsame Rubutowa
Bello Muhammad Danyaya
shkr 1 | 1001M9
==Buki A Ranar Fita Daga Gidan Yari==

Rubutu mai adireshi 1002M16 yana neman a ce wani abu a kan wata al'ada da yake gani kamar tana son ta kunnu kai a cikin Hausawa, watau tara mutane a yanka rago a yi buki don murnar fitowar wani daga gidan yari.

To, a ra'ayin kaina, ba ni ganin wannan al'ada marar kyau, saboda duk wanda aka sako nasa daga gidan yari dole ya yi murna, bisa ga al'adar dan'adam kuwa yana buki ne don nuna murnarsa, duk da yake wasu suna yi don nuna bakin cikinsu, kamar yadda wasu ke bukukuwan da suka shafi mutuwa, kamar Inyamurai.

Abin guduna daya ne, wannan abu kuwa al'adar ta yi karfi, don idan ta yi karfi za a tashi daga yanka raguna zuwa yanka shanu, inda daga nan za ta fi karfin talaka. Ina ma ganin ko tsayawa ta yi a yanka raguna za ta yi wa wani Bahaushe wuya, duba ga lokutan zanen suna ka ga misali. An ce a wani lokaci, wani mutum yana masallaci yana addu'u, sai aka ce masa an haihu a gidansa, maimakon ya ce "Alhamdu Lillahi" sai ya ce "Inna Lillhai". Ma'ana wata musifa ta far masa! Masifar kuwa ita ce neman ragon suna.

Ina gudu da tsoron kasancewa, a kama mahaifin mutum, maimakon ya rika rokon Allah Ya sa ya fito, sai ya koma rokon kada Allah Ya sa ya fito, don bai da abin sayen ragon bukin fitowarsa. Kada ka yi mamaki, haka yana iya faruwa kamar yadda aka ce ya faru ga wani Inyamuri da babansa ya cika.

An ce wai wani Inyamuri ne, yana zaune cikin Hausawa sai aka gaya masa mahaifinsa ya cika a asibiti, sai ya buga kuwa ya soma kuka, sai Hausawan da ke nan suka rika ba shi hakuri suna tausaya masa, sai ya ce masu "Kai ba fa mutuwa nake yi wa kuka ba, ina kuka ne, saboda baba mai kyauta mani ba. Baba bai tashi mutuwa ba, sai da ya ga ba ni da abin bukin mutuwarsa".

Wannan abin da zai iya faruwa ne ga Bahaushen da aka sako babansa alhali bai da abin bukin fitowarsa.

Masu nazarin al'ada su adana wannan.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124