Tsame Rubutowa
Kasimu Bello
shkr 1 | 1002M18
KALUBALE GAREKU HAUSAWA.

AL'ADUN MALAM BAHAUSHE.

Atakaice idan aka ce al'ada kowa yasan abinda ake cema al'ada.

Idan kuma baku sani ba to ga kadan daga dan bayanin nata.

Al'ada dai ita ce abinda mutane ko jama'a suka hadu suna yi ako da yaushe.

Ko kuma ako wane sati, wata, ko shekara, da dai sauran lokuttan da suke yinta.

MISALI;

Bukin sallar idi karama da babba.

Taron jiran afadi anga watan ramadana wato watan azumi, ko na salla a garkar sarki.

Taron suna da bukin aure da haduwa akan hanya atsaya agaisa da juna tsakanin manyan mutane, ko yaro yaga babba ya tsaya yagaisai.

Duk wadannan suna cikin al'adun malam bausahe.

Amma ahalin da muke ciki yanzu, al'adar gaisawa da juna idan an hadu tana gad da mutuwa.

Saboda zaka ga bama wanda ka sani ba. Ko kuma makwabci ba, a'a dan'uwankama idan ka gani dauke fuska zakayi, ko da ko ubanku daya.

Kuma wannan abu bai dace ba gaskiya abari wannan al'ada ta kwarai ta mutu.

Bayan zamanta al'ada addini ma ya yarda da idan kuka hadu da mutum ku gaisa koda baka sanshiba.

Idan ko har haka ne, to bai kamata abari wannan Al'ada ta mutuba.

Duba abin burgewa da sha'awa.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124