Tsame Rubutowa
Kasimu Bello
shkr 1 | 1002M19
INA MAFITA OLSA KE DAMU NA.

A halin da mu ke ciki yanzu, idan zaka yi aure kaje wajan budurwa. Akwai wata dabi'a ko wani hali wanda bai da makama bale tushe, ni a gani na. Wanda ya bulla tsakanin Uwar miji da Amarya.

A kwanan nan naji wannan abu, wato ga yadda abin ya ke.

A gidan su Mani aka yi wata amarya, ita wannan amarya matar wan Mani ce. Sunan ta luratu. A gidan su mani akwai uwarsu wato mahaifiyarsu. Da yaya nai Musa duk a gida daya su ke, to ita wannan amaryar wato luratu a ko da yaushe, idan mijinta musa ya dawo daga wajen neman na kalaci, wato abinda za su ci. Sai ya tarar da luratu a daki dunkule idan ya tambai ta mike damunta, sai tace olsa. A haka dai ko da yaushe ta ke shi ya rasa ko wace irin olsa ce wannan da kullum tana nan bata dagawa.

Sai sannan uwar musa ta yi tafiya wani kauye, wajen sati daya bata dawo ba.

Shi kuma musa sai yaga tun lokacin da mahaifiya tai ta yi tafiya, luratu bata koma dunkulewa a daki ba. Ko da yaushe ta na cikin walwala da nishadi.

Ya tambaita ya olsa ta ce olsa bata nan. Amma randa uwatai ta dawo daga kauye ranar luratu bata kwana ba sai da olsa.

Shi musa abin ya bashi mamaki kuma ya daure mai kai, ya rasa miye mafita ga wannan abu.

Kun san dan kirki shike shawara da uwayensa.

Sai musa ya je warin mahaifiyar shi, bayan sun gaisa sai tace mike tafe da kai dana. Sai yace shawara ta ce tami, yace game da matarsa luratu ta ce in jin ba sabani kuka samu ba. Yace a'a akwai dai abinda ya daure mai kai ya kuma shige mai duhu shina ya ke neman haske ko mafita.

Tace miye musa, yace luratu ce kowane lokaci sai ya cimmata a daki dunkule idan ya tambaita mike damunta sai tace mishi olsa.

Kuma shi ya kasa gano ko wace irin olsa ce wadda ke hana mata walwala ko da yaushe tana dunkule a daki.

Sai yace amma lokacin da kika tafi kauye ta samu sauki, ko da yaushe cikin walwala ni ka isko ta.

Uwar musa na jin haka sai tace to kada ka damu zan samo mata magani bada jimawa ba. Musa yace to ya tashi ya yi kasuwa wajen neman na na kalaci wato abinci.

Fitar musa ke da wuya mahairiyar su ta kira kane nai mani tace kaji abinda mu ka yi da danuwanka musa yanzu mika fahimta a wannan magana. Sai yace kamin yanke hukunci atab batar takwana.

Yanzu ki sake tafiya kauye kwana biyu mugani.

Sai ko ta daure kayanta ta fito tace ta yi wajen bukin wata 'yar uwarta a kauye, tana tafiya jin kadan sai luratu ta wartsake, ta tashi tana walwala cikin gida tana jin dadi.

Jin kadan sai ga ziyarar ba zata daga kawayenta su biyu. To daya daga cikin su kawayen na ta, mani yana son daya shi ko yana bakin darbejiya wato icen dogon yaro zaune a waje sai ya tsinke su tafe ko da ya taso ya cimmu su har sun shiga gidan sai kawai ya bisu ciki tunda gidan suna.

Ashe rabon ayi kashin sarki a gaban ido nai na.

ya shigowa sai yaji an fara cewa ashe olsa tayi kauye buki.

sai ya ja birki kamar an tsaida jirgin kasa da karfi.

Sai daya daga cikinsu tace baki dai bari ya san uwatai ce olsa ba ko, tace ai idan ina addu'a harda shi ke cewa amin.

Mani na jin haka sai ya koma watai bai ma isa shigowa ba.

Uwarsu na dawowa ya fada mata cewa hasashen haka ya ke don yaji da kunnen sa. Alokacin da kawayenta su ka tafo ya biyo bayansu.

Musa na tafowa uwar ta fadamishi, ya tashi zuwa rigima tace a'a mafita guda ku bar wannan gida kai da ita, tun bata kai ga wata fitina ba tun da tana sonka ni ce bata so mu zauna wuri daya da ita.

To kun dai ji abin da uwar musa tace, kuma kun gano olsa da ke damun luratu.

To ku wane irin hukunci kuka ga ya dace a dauka, kuma yasa matan yanzu ba su son zama da uwar miji.

kuma miye mafita ga wannan matsala ta ya ya za'a shawo kan wannan matsala a kuma walwaleta.

Muna jiran ku ba mu mafita.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124