Tsame Rubutowa
Kasimu Bello
shkr 2 | 1002M20
HAIFATESHON KA DAMU NA

INA MAFITA

An yi wani saurayi mai suna Musa, wannan saurayi ya samu kudi ya gina gida mai kyau.

Amma ya rasa mace wadda zata aure shi kai tsaye.

Ako da yaushe ya samu wadda ya ke so da sun dan fara zama, sai ta tambai yana da haifateshon.

Sai yace a'a da zaran an dan dade bayan ta yi bincike sai tace mai ta fasa aure nai.

Shi ako da yaushe abin na bashi mamaki ya rasa komi ke sa haka.

Ana nan wata rana sai ya hadu da wata budurwa, ya yi mata magana ta amsa mai, yatambayi sunanta tace mai Farida.

Ya tambai gidan su ta fadamai yace to shina nan tafe su yi magana.

Bayan kwanw biyu sai ya shirya yaje gidansu, da yazo kofar gidan sai ya sami yaro ya aika akirata.

Aka ci sa'a ta nan sai ta fito su ka gaisa, bayan sun gama gaisawa su ka yi magana tsakanin su ya fadamata shi aure ya ke sonta idan ta yarda.

Sai ko tace ta yarda ta amince, su ka ci gaba soyayya har lokaci mai dan tsayi.

Wata rana suna zaune suna fira, sai yace mata shi acikin 'yanmatan duk da yanema aure ita dai ce bai ji ta yimai wata tambaya ba.

Sai tace wace irin tambaya ce ya ke son ta yimai, sai yace bai ji ta tambai ko yana da haifateshonba.

Sai tace mi halam kana da shi, sai yace a'a bai da shi.

Amma yana mamakin yadda wadan can matan su ka ce ba su so nai don yana da haifateshin alhali shi ya san bai da shi.

Sai tayi murmushi, tace mai ai ba wai haifateshon na jini su ke maganaba.

Sai ya zabura yace wane iri su ke nufi halam.

Sai tace ai kana da mahaifi, yace awo.

Tace kuma yana raye, yace awo.

Tace to shine suke nufi da haifateshon.

Da jin haka sai ya buga kalma yace ashe mahaifina su ke nufi da wannan haifateshon in.

Sai tace ai idan kana da mahaifi raye shine mata ke ce ma haifateshon.

Daga nan suka yi sallama ya dawo gida yana ta mamakin wannan abu.

To miye maganin wannan haifateshon in.

Kuma mi yasa mata ke kiran mahaifin miji ko wanda zasu aura da wannan suna na HAIFATESON.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124