Tsame Rubutowa
Kasimu Bello
shkr 1 | 1002M21
BA'A HANAMA AYA ZAKINTA, DON GA ALEWA.

A wani gida ne ake wata rigima tsakanin UBA DA DIYANSA.

wannan yaro dai ya girma ya kai lokacin da ya kamata ace yayi aure. Amma sai dai bai da wada zai yi don bai da karfin da zai iya wa kai nai aure.

Shi kuma uban yana samun kudi saboda yana da karfin kasuwanci, akwai jari mai yawa garai.

Daya fahimci yaron ya na son aure bai iya wa kai nai cikin jari nai, kuma har ya fita da wani abu, sai ya kira yaron ya bashi gidan zama kuma ya yi mai aure.

To fa ana nan ba'a jima ba sai shi uban ya ga wata yarinya ya ji yana son ya aure ta idan ta yarda ta aure shi, don ya kai kamar shekara hamsin.

Ana haka sai ya dace yarinya tace tana yi, uwayen yarinya su ka amince su ma da zabin diyar su.

Sai dai ga wata matsala ta taso, matsalar kuwa ita ce shi wannan can yaron da yawa aure yana da kanne mata su uku, kuma ko wacen su ta isa aure.

Sai fitina ta barke cikin gidan Dattijo, rigumar kuwa ita ce su ba su yarda ya yo aure ba.

Kuma ma ace karamar yarinya zai aura wadda bata wuce sa'ar su ba, kila ma sun fita shekaru.

Rikici ko har gidan su yarinya, diyan ke zuwa su basu yarda akawo yarinya gidansu, kuma in ta yarda ta auri ubansu, zata ga ba dadi.

Dattijo yabi ya rude, yana son aure, diya nai sun haddabai da rigima. Ga kuma uwar su na kama mu su.

Dattijo ya hasala ya kira kowa da kowa, ya fara da cewa.

To fa ku sani ku ma su rigima, ba za'a hanama aya zakinta ba, don ga alewa.

Sai can uwar yaran ta mike ta ce, ai ko dole a bari har a shanye alewa sannan a sa aya a baki.

Sai shi dattijon ya ce, to ai ayar zata iya bushewa har zakin ta ya fita, kamin alewa ta kare.

Sai uwar yaran ta ce aiki sai dai ta bushe ta rasa zakin.

Kamin dattijo ya yi magana sai can wata daga cikin diya tace

Baba wallahi baka yi mu na adalci ba in har ka auro karamar yarinya.

Kawai sai su ka tashi su ka bar dattijo cikin tunanin wannan magana ta rashin adalci.

Shin anan waye ba'a wa adalciba, Dattijo ko Diyan na shi, shi dai aure ya ke so.

Kuma ya samu mai so nai karamar yarinya, su kuma diyanai ba su son auren.

To wa aka wa rashin adalci, shida Allah bai hana mai auren ba, ko su da ba su samu mazan aure ba, har uban su ya shiga sha'awar karin aure

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124