Tsame Rubutowa
Kasimu Bello
shkr 1 | 1002M22
AN YANKA TA TASHI

Wani barawo ne, wanda ya shahara wajen iya sata, ya haddabi mutanen garin su.

Ana nan ana nan, sai dai wata rana ya shiga kasuwa wajen yin sata, sai ya ga wani dattijo dauke da jaka a kansa.

Yana gani nai sai yace tsuntsu daga sama gasasshe, kawai sai ya shiga yin 'yan dubaru irin na su na barayi.

Ya ci gaba da biyar dattijo da sannu-sannu sai da dattijo ya zauna wurin wata ita ciya don ya huta, sai kwana ya kwashe shi.

Da ya yi kwana sai ya lallabo ya dauke jakar dattijon, bayan ya tafiya tai sai ya isa gida ya kai ma matatai jaka su ka buda su ka ga kayan mata da kudi a ciki, sai matar ta yi ta murna ta samu ka ya shiko sai ya dauki kudi.

Ana haka sai su kaji sallama a kofar garka.

Koda shi barawon ya fito don yaga mai sallama, sai yaga dittijon ga da yawa sata, sai ko ya yi karfin hali suka gaisa.

Kasan barawo da karfin hali kamar karen da zai mutu.

Bayan sun gama gaisawa, sai yace lafiya dai ko dattijo, sai ya ce kalau ba kalau ba,

yace mi ya faru halam, sai yace ba aiko ni aka yi da kaya in kawo ma matar gidannan sai dan kwana ya figan a bakin ittanya, ko da na tashi an dauke.

Ita kuma matar dama ta biyo shi a baya don tana zaton kamar ma su kayan ne su ka biyo shi.

Tana jin haka sai tace kaya a kawo ma matar gidannan.

Kawai sai ta fito garka, tana fitowa sai taga ashen kanen uwarta ne ya yi sallama.

Suna hada ido sai yace ga ko tanan ta fito, sai su ka gaisa.

Ya kara yimata bayani irin wanda yawa mijinta, sai tace ai babu komi haka Allah ya kaddara rabon mutum bai tsere mai.

Bayan ya huta, sai suka yu sallama da shi ya koma.

Bayan tafiya tai sai dai matar barawon ta ce mai.

To fa an yanka ta tashi, sai yace ai dama tasassace.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124