Tsame Rubutowa
Kasimu Bello
wt 9 | 1002M28
AN FARA BA A SAN RANAR KAREWA BA.

Awasu lokuntan baya ne, aka yi wani gari mai suna YA AKA YI. Wannan gari dai yana da yawan Jama'a ko in ce mutane.

Garin kuma yana da yawan Albarkatun kasa, dai Babbar matsalar garin shine, bai da shuwagabanni na kwarai. Daga kan Maigari har zuwa Fadawansa duk bana kirki bane.

Asalima asa masa wannan suna na YA AKA YI, saboda walar da Talakawan garin ke yi. Sunan da ake cema garin ada, shine "BAKU DA RAGGO" saboda yawan aikin su da Albarkatun da Allah ya ba su. Sai dai gashi ya samu canjin suna sabosa rashin Shuwagabanni na kwarai.

Idan kana da gona mai yawan hatsi ga damana, to dole ko ta zama ta maigari ko kuma kuraba hatsi idan ka gama girbi.

Bayan su kuma 'yan fada nada nasu kaso. Haka dai komi kake Sana'ar sa, su na da nasu kaso.

Ana haka sai wata fitina ta bullo kai tsaye waton barayi, su kuma suka shigo garin idan baka basu kudi ko kaya ba to za su kasheka, ko kuma su jima rauni.

Da suka ga ba su samun wani abin kiri sai suka koma suna daukar mutane su ce akawo kudi ko su kashe mutum. Idan ba a kai ba za su hallkashi.

Abin dai yawa garin Ba ku da raggo yawa, suka rasa miye mafita. Sai suka taru suka yi mitin su ka ce su suna ganin duk wannan abu dake faruwa saboda wannan maigarine da fadawansa.

Ana cikin wannan mitin sai ga barayi sun shigo garin sun kawo hari. Aiko sai kowa yayi ta kansa, bayan sun koma daji sai aka koma taruwa aka yanke shawarar aka kashe maigari don da saninsa komai ke faruwa. Ba a yi watata ba, kawai sai kowa ya koma gida ya dauko abin da ke garai na fada.

Wasu abin bugu, wasu kuma takobi, wasu wuka, wasu tabare da dai sauransu.

Kamin ace ha gari ya bare da fitina an taru gidan maigari sai akashe kowa ke cewe, kamin minti goma an kashe maigari da fadawansa. Wasu da suka sami labari kamin azo garesu sun gudu.

Bayan kwana biyu kuwa sai ga barayi sun koma shigowa, aiko mutanen gari sai suka fusata, kowa ya fito da makamin da ke garai. Aka daura rigima da bariyi, gashi makaman barayi sunfi nasu. Amma dai sun kokarta iya yinsu. Har sai da suka samu galaba ga barayin.

Su ko 'yan'uwan barin da suka ji haka sai suka kawo hari cikin dare, suka yi kan mai uwa da wabi, kai har sai da yazan idan mutum ya hadu da dan uwansa bai ganeshi. To daga nan fa gari ya rikice babu maigari, kuma ga mutane sun halaka. Garin ya zama abinci ma wuya ya kai wanda mutum zai ci. Idan an hadu sai kaji mutum yace ma dan uwansa ya aka yi, shima irin wannan tambaya zai yi mai in shi yariga yi. Ahaka dai suke cikin mawuyacin hali, ko ina suke sai kaji suna tambaya ya aka yi, har aka mai shesu mutanen ya aka yi, maimakon garin baku da raggo. Haka sukaci gaba da zama babu maigari babu kwanciyar hankali, babu abinci.

Allah shi taimaka muna ya muna kariya da tsarinsa.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124