Tsame Rubutowa
Kasimu Bello
wt 6 | 1002M30
Amsar tambayar wani memba, daga wannan gida. Mai lamba 1060M15. Yana tambaya ne akan garurun 'yan dambe.

To ga amsar

Na farko dai garuruwan da ake kira kudu sune kamar haka.

Kano, Kaduna, Zariya, da Daura.

Su kuma wadan da ake kira Arewa, sune kamar haka.

Katsina, Zamfara, Kebbi, Funtuwa da Sakkwato.

Sannan kuma maganar da kayi ta Kurumada, To abinda dai jama'a suka sani, shine Gurumada.

Kuma su wadannan Gurumadan, Fulani ne daga birnin Kebbi. Sune ake kira da Gurumada ba Kurumada ba.

Dafatan mai wannan tambaya. Zai gamsu da wannan amsa.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124