Tsame Rubutowa
Kasimu Bello
wt 6 | 1002M31
BARAYI KO MASU DAUKAR NASU.

Wani garine mai yawan jama'a da albarkatun kasa. Mutanen wannan gari suna iya kokarinsu wajen neman na kan su. Sai dai matsalar basu da jagora na gari. Idan masu kudu suka bada zakka aba marasa galihu da musakai, sai shi wannan jagora ya hana su. Iya ka ya samu mutane kalilan, ya basu abinda bai taka kara ya karya ba. Gashi kuma duk wanda zai fidda zakka dole shi zai ba, don shine jagoran jama'a. To ana haka kwanci tashi, sai musakai da marasa galihu, suka fara gajiya da wannan jagiranci nashi. Suka fara kai kara ga masu bashi zakka don su san abinda ake ciki, ina sai dai yunkurinsu bai yi nasaraba.

Suna cikin wannan hali sai wasu daga cikin mutanen suka yi shawara. Suka ce idan ya san wata, ai bai san wata ba.

Su bari sai da damana tazo yayi aikin noma mai yawa, ya samu amfanin gona mai yawa. Ga kuma na mutane da suka kawo don aba jama'a.

Lokacin rabo yayi, ya kira 'yan dai dai kun mutane don yabasu wada ya saba yi, ya rike saura. Sai yaga dimbin taron mutanen da bai zata ba. Hankalinsa ya tashi ya na tunanin waya kira mutane haka. Yana cikin wannan tunani bai ankaraba. Sai yaji ana cewa kar ku bar koma anan ai duk namu ne. Mutane sun shiga kwasar kayan da aka kawo har da ma nasa da ya noma. Kai har gidansa ma sai da aka shiga aka kwashe komai. Aka kuma nufi gidan magoya bayansa suma aka kwashe na su. Abinda mutanen ke cewa ai duk kayanmuna mu kwashe.

Shin jama'a wadannan mutane dagaske kayansune, ko kuwa na jagora.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124