Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M103
====DABE A KASAR HAUSA==

MENE NE DABE?

KALMAR DABE: Dai kalma ce mai dau ke da manufofi daban-daban. Misali ya daba masa wuka.Ya daba laka.da sauransu.To wannan rubutun dai za ya yi bayanin Daben da ake yi na dakin mata kamar in za a kai amarya. ko angina sabon daki.

DABE

A da ni na san a kauyukan mu ana toron Dabe. Matane ake gaiyata daga unguwanni daban-daban. Ko wace da madabi.Wato abin yin damen. Zaka gansa da mariki silili da baki mai fadi. An sassakashi an yi masa yar lankwasa,kamar cokalin icci,amma shi ba a yi masa zurhin dibar abinci ba. Ya na da tsawo kamar kamu daya,ko ince tsawon bakin gauwar hannu zuwa karshen yan yatsu. To amma kamar yada na ce shi dan lankwasa shi a ke kamar dai wukar nan ta masu ginin zamani(Ginar Bulo) amma shi ba karfe ba ne. Masassaka ne ke sassakasa.

To bayan anyi taron da galibi wani karo an fi yinsa da safe zuwa azzahar ko zuwa la,asar. Kafin sannan an dabe daki. Ana daben ana rera waka kamar haka:

"Mai rowa ta yi gaiyar dabe,

Ku dama mata badun halinta ba"

Haka za su rinka rera waka suna Daben har su kare.

KAYAN DABE

Tsakuwar Burji.

Ruwa

Ruwan dorawa don kasar ko tsakuwa ta yi tsauri.

Madabi da sauransu.

Za mu ci gaba.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124