Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M104
====FATAN ZAMA LAFIYA===

A kumyace na ke mika sakon fatan alhairi da zaman lafiya mai daurewa da bada zuriya tsaiyaba ga wannan muhimmin Auren da za a daura na dan MAKARANTAR HAUSA. Watau abokin haihuwa ta KASIMU BELLO. Saboda nisan da na yi ga zuwa daurin Auren.

Kumyar da na jiya ita ce wai na kasa, ko wani ya kasa yin rubutu akan wannan auren. sai da mahaifin mu ya yi da kansa. Anan ne na ga rafkanuwata. Amma ga tsaraba ta.

Bismilla Allah,

Sarki mai falala,

Ban iko jalla,

In tsara kafiya,

Wannan da na wa sahibai=Haba!haba!!

Ya rabbi rahimi

Ka haskaka hadimi,

Muhammadu katimil,

Na biyul rahimil,

Ka dauka aurennan,=Haka!haka!!

Amartu da ango,

Abinda na hango,

Ku ma ku hango,

Taro na ango,

Da Amartu ta dango,

Duk kanku anka yo= haba!haba!!

Ki tausaya masa,

Ki gurfa na masa,

Abinci ki basa,

A ma baki nasa,

Bar nuna kasiya.=Haba!haba!!

Malam kasimu,

Na sanka karimu,

Sannan kuma kamimu,

Damke ta ka samu,

Farin ciki.=Haba!haba!!

A nan zan dan tsaya,

Yan tsurku ku dan yi ritaya,

Allah ka yi kariya,

Ga auren nan.Haka!haka!!

Roko na Allah,

ka kauda matsalaa,

Kara mini fitila,

In zarce yan uba. Haka!haka!!

Ya Allah ka ba da zuriyar da za ta zama madaukakiya. Anan Duniya da ranar kiyama.

Malam kasimu a ci anganci lafiya. Sai Allah ya mai da ni,na zo ganin amaryar dan uwa na. Amma kar a manta da mu,a yi mana addu,ar cimma irin wannan ranar. Kuma addu,ar don Allah ta kasance alokacin da ango da amarya sunka kare raka,o,in nan biyu. Da fiyayyen halitta ya umurce mu. Allah ya sa a yi lfy,Allah ya bada zama lafiya. Amin summa amin.

Baban mu maganin kukanmu. Barka da wannan ranar. Allah ya karama lafiya. Allah ya daukaka MAKARANTAR HAUSA.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124