Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M105
===GWAURON KIDI ZUWA GA GWAMNATIN KANO===

A yanzu na ga wani labari a shafin BBC Hausa. Mai bayani akan korar almajirar tsangaya.

To gwamnatin kano in ana sara arinka duba bakin gatari. Ka da Allura ta tono galma. A samu ko matsala don ciko sai ya biyo gyartai.

Abin da na gani ga gwamnati dama saraki da masu madafun iko na jahar Kano. Da ma duniya baki daya shi ne: Yan siyasa da saraki su kama kansu da shiga hurumin malammai na ko wane sashen addinin musulunci. In dai ba fitina sunka zo da ita ba.Saboda keta huruminsu ba karamin hatsababanci da raina Allah ba ne. Mun sani Allah fa ya fada "Duk mai fada da waliyinsa, to da Allan ya ke" Fada da Allah ko ba riba wallahi.

Wai hadda ikirarin an kamo almajirai 21 kamar wasu barayi. To mu dai mun san da wallahi ko mutum anka ce ya zauna kano, ya samu shekara a ciki bajahili ba ne. Koda ko ba karatu ya ke ba. Ballai mai karatu. Duk duniyar da mai karatun Allon kano ya je ba za a kirasa jahili ba. In ko mutum yayi boko kamar musta kyam-kyam. Wallahi almajirin tsangaya ya fi karfin wula kantassuwa ga kowa balle a jahar kano da abin gado ne. Kamar Sakkwato da Gwandu da dukkanin kasar da tutotin shehu mujadadi suke. Saboda haka mutum ya daina ganin yana bisa mulkin shekara hudu ko takwas,wa su su rinka zuga shi yana cin zarafin bayin Allah. Ku kore su,saboda baku son kuji ko ku ga garinku na walwala da ci gaba. Kun manta da in kunka tashi neman mukamin su kuke iskewa su yi muku addu,a. Kun manta ko saukar kur,ani nawa kunka sa a yi muku da kuna neman mulkin. Wallahi kunza ma kaji. Masu ci su goge baki. Kuma in kunci kowane baki kun goge,kun kwashe lafiya. Ina gaya muku banda wannan. Ku kiyayi wannan al,amari. Ku barsu su yi abinsu. Kusan fa shekara 7 kuna ta wannan borin, sai a yanzu ne shaidanin aljaninku ya hau. To ku yi kokarin yi masa girka, tun dare bai yi mu ku ba. Ina ma da ace dauke nauyinsu kunka yi. In babu lauje a cikin nadi.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124