Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M107
===TAKA TSAMTSAM===

KALMAR TAKA TSAMTSAM:Kalma ce dà ke nufin yin tsantsaini KO bi a hankali a bisa ga lura ga KO wane sashe.

IRE-IREN TAKA TSAMTSAM

A nawa râ,ayin Taka tsamtsam ya kasu zuwa gida biyu. Kamar haka

1. Taka tsamtsam na duniya.

2.Taka tsamtsam akan abuwan lahira.

1.TAKA TSAMTSAM NA DUNIYA: Wannan taka tsamtsam ya na Nuna yada zaka zauna da mutane da aikinka da sana,arka da sauransu. Wannan ya na nufin yada zaka tsara lamurran kasuwancinka. Yadda za ka samu mafita. Haka aikinka. Misali. Idan kai tela ne a wajen yankan yadi saï ka yi taka tsamtsam. Ga awon da ka yi. Kasuwa kuma saï ka yi taka tsamtsam don kada ka rufta riba ta shige a cimma uwa. Da sauransu.

2.Taka tsamtsam na lahira: Shi wannan taka tsamtsam kusan ya kandame na daya. Saboda idan ka duba shi ya na ma magana ne akan hadisin da ke cewa"ku yi wa kanku hukunci,kafin a yi muku"To shi mumini a komai nasa taka tsamtsam ya ke. Misali ka yi taka tsamtsam wajen ibadarka. Ka yi wajen sana,arka. Ka yi wajen aikinka. Ka yi wajen kallonka da jinka. Dasauransu.

Kadan kenan atawa fahimta. Ku kara min ilmi. Don Allah.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124