Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M108
===MAYANI===

A yankin sakkwato da kabbi da sauran yankunan Zamfara suna kiransa mayani. A katsina da Kano da Kaduna su ce lalita.

Shi mayani tsohon abin ajiyar kudi ne da tsofafi ke saka kwabbai KO abin da ya sha fi karfe na kudi. Don in an sa su ga aljihu ya na iya hudewa kudin su zube,bâ a sani bâ. Galibi yanzu an daina amfani da shi a najeriya. Amma anan nijar da janhuriyar Bénin da na je na ga tsofafi suna amfani da shi. A yanzunnan sha biyu saura ina kasuwa na ga wani tsoho ya fidda shi. Saï ya tuna min da kaka na,Allah ya jikansa. Idan na zo ansar kudin man makarantar Allô,in bai da su saï ya fidda mayaninsa ya ce" ka ga mayani na komi bai da,yi hakuri har a samu"

=== Hare-haren Alabai ga mayani====

Alabai ya kai wani harin nokiliya ga mayani,saboda a yanzu KO a inda ake samun kudin karfe sunfi amfani da alabai. Wannan kowa ya faru ne don samun cigaban da anka cimma ta fannin kere-kere da sake-saken zamani. Saboda yanzu shi alabai kana iya samun mai Aljihu biyr koma ma fiye. Nan kudi nan idikati nan zato(kudin karfe,coins)da sauransu.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124