Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M113
===KU KIYAYI TABA MUTUM UKU===

Ni anawa gani mutumci ya fi komai. Duk wanda kasan in ka tabasa,zai iya cin mutumcinka. To ka kiyayesa. Sai a zauna lfy ya fi.

Akwai cin mutmci da dama, da mutum ke iyawa mutm dan uwansa. To kirana ga masu katsalanda a sha,anin mutane da su daina taba mutum uku. Wata kila sai ka ce da ni suwaye mutum ukun nan? To mutum ukun nan sune:

1.Malami

2.Mawaki

3.Marubuci(dan kartakwana)

Kasan dalili na?

Dalili na shi ne:wadannan mutum ukun;suna da hanyoyin kasheka da ranka.irin wannan mutuwarko. Da yin ta gwara mutuwar gaba daya. Saboda duk inda mutumcinka anka ce ya zube. To wannan zubda mutumcin na iya biyarka har diyanka da yayanka. Kamar yada mutumcinka ke daurewa ga har jikokinka.

Abin lura ga wadannan mutum uku shi ne: Ba su taba ka sai in ka tabasu.Saurari sani sabulu.

"....Hadiza ciya leda,

Bari jana hwada,

Ke san kaunata kike,

Sannan ni kuma wanki ne......"

Kaji ya gargadi hadiza ciya leda.

To bari ka ji inda ya yi cin mutumci. A cikin wakar mai dadiro

"......Mai daro batacce ga Allah,

Mai dadiro kana da bakar fita,

Kuma kana da koshin talauci....

Karawai ban hanaku yin dadiro ba,

In kunka ta shi yin dadironku,

... Ku ne mi nakirki ...

Ga dori can ban kula da mai dadiro ba,

Sai ma su dadiro sunka ja ni,

Ni ko na kama zancen halinsu,

Saboda Nana! Shin wace nana?

Shugaba Nana yar yaka naye,

tantabara uwar alkawari,

Komai dare gida kika kwana,

Nana ba ta kwana a daji.

To kadan, cikin kadan na cin mutumcin da Alhaji Sani Sabulu yayi wa masu dadiro.

Mawaki kenan.

Sai malami kana iya sauroron mai guduma,Kabiru gwambe, Abduljabar Malam nasiru Kabara. Da sauransu. In anka taba su dukkan wadannan suna yin raddi. In ka taba su.

Kashi na karshe da ko alkali na tsoronsu, ballai gwamnati da yan siyasa da saraki da sauran masu rike da madafun iko na kowane sashe. Sune yan jarida da marutan littafai.

Karamin misali shi ne gyaran fuskar da wakilin Leadership Hausa a Sakkwato Sharfaddeeni umar yayi wa kamusun karen maganar Hausa. Watau kura-kurai dubu da daya. Kuma ka ko ma tsallakawa ka karanta Anbaliyar kura-kurai a tekun labarai.

To shi dan jarida da marubuci kowa na yi da su,dole.

To ku fi maida hankali ga wadannan mutum ukun. Ba su tabaka,amma in ka yi ma lamirinsu karan tsaye. Kana kwasar kashinka a hannu. Musamman yan jarida. Sun ma fi duk wanda ba su ba hadin kai. Kuma duk wanda ya taba daya da ga cikinsu a duniya. Sai sun ya da sa. Kamar yada su ke yada labaru.

A kula. Wannan gabatarwa ce. Zamu kara ba gaba. Muna kuma neman karin haske da shawara.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124