Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M114
====KASHIN BAUNAR BULAN YAKI===

Muna jin ana cewa kashin Baunar Bulan yaki. To a kwai ra,ayoyi da dama, a game da wannan ra,ayin. Bincikin da na yi ga malammai na a gida.

Kamar su malam muktar sahabi, malam Tijjani Balarabe,Malam Muhammed usman (Malam Gide BCE jami,ar kano.) da malamina kuma maiyakin Gora ta Gabas.Ga yada sunka ce:

" Ga yadda sun ka ce: Mutasa ne guda shida, daya shiyar gabas,daya shiyar yamma,daya shiyar arewa,daya shiyar kudun garin. Daya tsakiya, daya kuma daga wata shiya. Sai hira ta kama su. Sai daya ya ce yanzu dai bauna ta biyo, mu kasheta. Da kai wane sai abaka kafar gaba. Kai kuma wane abaka ta baya. Ni kuma ta baya. Shi kuma wane aba shi ta gaba. Wane da wane aba su kai da hanji. Ganin an yi kwaruwa a cikin rabon sai wadanda sunka sami kai da hanji sunka ce . Wallahi ba su yarda ba. Tun anan cacar baki, har aka kai ga dukan juna. Daga nan fa sai kowa yazo sai ya shigar ma yan unguwarsu. Ai sai gari ya rikice. Sai mai gari ya jiya. Ya tako kafa da kansa. Ya tsaida fadan. Sai ya nemi mene ne mafarin fadan daga dattijawa, sai sunka ce masa sun iske ana dukan mutanensu. Sai sunka kama. Sai ya ce akan me? Babu ansa. Sai ya kira matasan. Sunka yi masa bayanin yada abin ya faru. Sai mai gari ya ce ina Baunar? Sunka ce bata ma biyo ba ranka ya dade. Sai mai gari ya ce maganar banza. Ka ji KASHIN BAUNAR BULAN YA KI.""

Amma ta na iya yiwa wani ya samo wani karin bayanin da ya ji shi kuma wanda ya sha ban-ban da wannan. Sai a taimaka a kara muna. Saboda wadannan magangannun suna da kyan sani matuka. Na gode.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124