Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M115
===MANYAN MAYAUDARAN ADUNIYA===

Wanda na ke ganin babban mayaudari shi ne mai soyayya da macce fiye da daya. A bangaren mata kowa maccen da ke soyayya da namiji fiye da daya. To ni anawa ganin Namiji ko macce duk wanda ke soyayya ba ta yaudara ba. Ko maccen da ke soyayya ba ta yaudara ba. To ya tsaya ga daya.

Saboda masoya maza in sunka yi miki yawa,akwai mai wata manufa ta gurbataki. Kuma kwadayin abin Duniyarki ne ya ja miki. Gurbatawar na iya ta kasance ta yaudararki don ya yi zina da ke. Ko don cimma wata manufa tasa.

===Abinda zaya biyo baya==

Idan ya sadu da ke ta hanyar zina! Ya cuceki,ya cuci wanda za ya Aureki, ya cuci mahaifanki, ya cuci danginki, ya cuci zuriyar da zaki haifa, tun daga gareki har tashin duniyar zuriyarki. Haka a lahira Azaba na can tana jiranki. Saboda haka mata ku kula da wayannan mazan. Duk namijin da ke sonki, to ya same ki a gidanku,da sanin iyayenki. Da sanin iyayensa. In ma ya taba zuwa to in ya zo yau, ki ce ya turo. Kawai ki gani. In ba da gaskiya yake ba, bai sake dawowa.

Ku kuma matan da iyayensu sunka tsada ma mijin Aure ku kamar an tanka baka ne. Kuma wannan bakar ta harbi ce,harbin ma,ana biyu gare shi.

Ma,anata farko zuwa gareki:Dalili na anan shi ne alokacin samari ke ta kusantarki. Saboda sunsan sun ke tare siradin cewa " su turo" abin da saurayi ya ki jini a duniya. Amma mugu. Don haka zaki ga suna ta zowa. Ke kuma ana ki tunani aduniyar nan ke kowa sonki ya ke tsakani da Allah. Sai an kai ki an baro. Sai kowa ya watse. Ki gane Borno gabas take. A wancan lokacin da ki ke yanke sakarki ta masoyiyar kowa. In wani ya yi miki nasiha makiyinki ne. Amma a yanzu kina ma neman mai hirar zagi ko kin mayaudaran masoyanki. Kamar yadda ya faru ga sharwatu. Sai kuka da da na sani. To ai yanzu an sani ko?

Ma,ana ta biyu kibiyrnan na iya komawa ga reku ku biyun. In ba ku iya kanku ba. Duk kibiyar tana iya wannan bala,in ga kowa.Yadda kibiyar zata soki namijin shiko za ya koma bangare daya yana shan shagalinsa. Da da in anyi auren miji dan sharholiya mata haka. To kaga Jamilu ga jamila ai duk suna ne.

Shi ya sa na kira su ma yaudaran duniya. Abinda na fada ga macce haka ne ga Namiji.

Ni dai gani na a yi haka. In kum yarda.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124