Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M128
====KO ANA TA JAKI,BA A RASA TA TAYYIKI===

Ko ana maganar corona to ana ta Hausa da Hausawa. Saboda naga duk halin da ake ciki na matsalolin rayuwa ana cinkasuwa,koda kadan ne. Ana cin abinci, ko babu dadi. Ana,ana. Duk kuma a wannan halin. To meyasa ba a maganar Hausa da Hausawa. Mu yi abinmu kamar yadda anka saba,ko mu dan kwatanta: "ku rika min yaya,

Kowa gaji baisaba,...

Aikin mutum ya bar shamai kai

Don kar a gane banasa ne ba,....

Allah mai girma

Ya zilzilalo mai ikon kowa,

Shi kadai kawa mutum yadda yaso" Alhaji sani sabulu,Kanoma.

Don haka muna addu,a muna aikin mu. Amma ace ga wani abu da zaya hana mu wannan gwagarmaya. Sa buzun sa. Shi fa sabo ne, mu kuma mun kwan kan hanya. Muda iyayenmu. Shi da ko iyaye baida. Ko akwaisu ko sun boye. Kada mugun aikin cutar corona ya hana mu kyakkyawan aikin Hausa.Don Allah mu yi na mu, mu yi nasa. In ya zama me muna dole.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124