Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d~gora)
shkr 1 | 1009M134
===SO!SOYAYYA!!!KAUNA!!!!AMINTAKA!!!YAN UWANTAKA!!!!===

Jama'a ga tambaya ta. Wai a yanzu akwai wadannan? Saboda ni dai na ga kusan mutane ba su da mu da su ba. Kowa ya ki halas da haram ya ke,sai kalilan. Musamman a fánnin samari da yan mata. Yaudara kowansu ya maida ta kawa. Shi ne na ke tambayar anya ko wadannan abubuwa wannan harin na barinsu. Don fa ina ganin ya ci zarafinsu sosai. Da ga karshe ma ni ina ganin kamar anya soyayya a tsakanin samari da yan mata ko ta aure ce ba ta kusa zama gawa ba. Saboda in kabi maganar malumfashi,(2007),mujallar makarantar Hausa.

So+so= soyyaya: wannan ya na da wuyar samu. Sai dai galibi So+ki= so kiyayya. Atakaice kenan

Wanda ya sha wuyar abu, galibin rayuwarsa ya kan yi fatali da wannan abin.

Kada ku ga laifi na akan wannan ni gaskiya ina tambayar kaina wai shin akwai wadannan abubuwa, abisa tsakani da Allah?Don Allah wani ya waye min kaina. Ina cikin duhu ba na shekara bakwai kenan. Don Allah a faiya ce min.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124