Tsame Rubutowa
abubakar m. damma(a.d.gora)
shkr 2 | 1009M14
KU FAHIMCI BAHAUSHE YA KU MAKAFI

Karen magana fa ba magana ba ce kara zube.

Masana da dama sun yi bayanai da rubuce rubuce akan karen magana.Galadanci(....) "Karen magana wani dunkulallen zance ne wanda sai an hau buzun karatu sannan ake sanin ma,anarsa". Bunza,A.m.(2006) "KAREN MAGANA kamar hadisi malam Bahaushe ya dauke sa,ba ya fidda sa sai ya tabbatar da abin".(Watau sai yayi ta gwada shi da mai-maita sa. Kamar yada Malam Bello MH ya yi ta gwada kayan MH. Sai da ya tabbata sun yi sannan ya fitar da su. Haka Bahaushe yayi kuma yake yi acikin al,adunsa.Ko ba ka dauki bayanin Bunza ba. Ka saka na ka dan hankali ka kalli duk wani abu na Bahaushe. Ba kara zube ya ke yinsa ba. Sai ya sa kimiya,hikima da fusaha da falsafar ilminsa.

Yada zaka tabbatar da Bahaushe kamar hadisi ya dau Karen magana: Bari sai Bahaushe za ya yin abin assha. Sai ka yi karen maganar da ya danganci abin.Za ka ga jikinsa ya yi sanyi. In mai kyau ne kuma za kara masa kwarin guiwa. Kamar dai ka karanta masa hadisi. Ni na gwada.

Duk abin da Bahaushe ke da ya na da karen magana akansa. Ba makaho ko gurgu ko kuturu ko kurma ko bebe ko wani nakasashe ba. komai. Misali:Ba a wane bakin banza.Abin nema ya samu matar dan kabo-kabo ta haifi Babur.Duniya gidan kashe Aho. In bubu rame me ya kawo maganarsa"inji makaho" A dade ana yi sai gaskiya. Kurciya dangin HAUKA. Yaro ba mutum ba,sai ya girma. Shi ba ma mutum ba ne. In su nakasa su anka yi. Ku yi hakuri maka fi . Ni na fi ganin kiranku a kalmar NAKASASU tafi muni bisa duk wani karen magana.

Ku na da baiwar da wani mai ido bayada. kamar yada Malam Aliyu Na Mangi ya ce a imfiraji"...Zuciya in ta makabce,ganin ido ba zai yi fa,ida ba"

Kura fahimta duk mutum dan tara ne. Kowa na da tasa matsala. Ban da shugaban halitta Annabi Muhammadu(S.A.W)

Baiwarku: Idan anka haifi yaro da makafta zayyi ta abubuwan ban mamaki Ka binciki tarihin Aliyu na Mangi. In daga baya ta kama sa watau tsufa ko wani iftala,i,Allah ya jarabce shi,kuma za ya ba shi lada mai yawa.

Kada ku damu da karen maganar da ya shafe ku. Karen magana ya shafi kowa da kowa. Ku rinka nazarinsa in kun ji shi. Da yawa sunan abu ka fitowa a cikn karen magana, amma manufar ba anan ta ke ba. Misali Ba kullum ta ke salla ba. Da sauransu.

Ina jiran gyara ko korafi


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124