Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M20
YAR GAGARA TASAMU MATSAYI MAI GIRMA A ABUJA

Wani labari na gani a shafin BBC HAUSA mai taken:

"KARUWANCI BA HARAMUN BA NE A ABUJA= KOTU

Wai wata kotu ta sa a biya diya ga 16 mata masu zaman kansu( karuwai) don anka ma su an tsare su. Saboda babu wata doka da ta haramtasa.

Mai shariya Binta Nyako, ce ta yanke wannan hukuncin a babbar Kotun ta birnin tarayya Abuja.

Lauyan da ke kare Karuwai Baba Tunde Jacob wanda shi ya yi ruwa da tsaki akan matsalar.

BBC ta bayya na a watan Mayu na 2019 an kama mata 60.

To anawara,ayin: An yi wagegen kuskuren bayyana wannan hukunci abin kazanta. Tirr! Da wannan abin sabida kace na cen da za ya kawo. Bayn haka akwai matsalolin da za su faru a kasa kafatan. Ba a babban birnin tarayya kadai ba. Masalolin

1. Duk yar gagara zata buga kirji gaban kowa ta fadi aikinta. Saboda babu wata dokar da ta hana ta.

2. Kangararrun mata za su fantsama a kasa.

3. Yayan banza za su kara yawa.

4. Cutar yoyon fitsari zata fantsama ga su karuwan.

5. H.I.V ya kara samun matsugunni.

6. Ku kuma matan aure ku ta hakuri. Musaman masu mazan da basu iya kyale kishirwa.

7. An manta da shari,ar musulumci.

8. Sata da yawon dare za ya kara yawaita.

9. Yan fashi da ta ,adanci da zubda jini.

10. Bala,uka za su kara fantsama.

Ina ma dai cewa anka yi su yi aure,watau gamnati ta auratar da su,ai ya fi.

Wani misali a yamai( Neamey) Su yar gagara suna daurewa yan sanda kai. Bayan su ma aikata sun kare sintiri a cikin Dare. Su kuma su yar gagara su fito bayan sallar Asu ba. Su rinka shiga Dakuna suna sata.Duka ba a yi sati uku ba wata ta shiga dakin wazu Alhazai ta kwashe musu wayoyi. Ana mu shavon ma wata ta shiga ta tsame aboki na Umar. Da anka kai ta ga yan sanda wani daga cikinsu ke cewa" kwanan baya ma an kawo ta, da mari a hannunta ta gudu" Bayanin daure kai da ya bijiro ga bakiin D.P.O ta fito.Baki na da nasa yake gayamin haka.

Kalmar yar gagara da na ce ana samun sa a cikin littafe mai suna FASAHA AKILIYA na Dr. A.A jegga. A cikin wakar YAR GAGARA.

INA JIRAN GYARA KO KORAFI KO SHAWARA.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124