Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M22
......FASHIN BAKI.......

Na ga wani rubutu da edita ya yi,inda ya ke neman cewar wani abu daga dalibbai da malamman .wannan gida mai albarka da tarin ilmi. To duk da nasan sha,anin MALAM sai dai ka dan yi iya iyonka ka fita(maliya ne) kowa na mamakin al,amarinsa.Duk da haka ni zan dan gwada ko zan iya. Duk da na ke ko alkalami ban fara iya riko ba a wannan farfajiyar zan gwada sa,a ta. Bahaushen karen magana na cewa"Da koyo akkan iya". Ina tsoron kuma karen maganaarsa da ke cewa" Da mugunyar rawa gara kin tashi".

editan ya zaiyano wakilin suna guda shida kamar haka

1. Karami

2. Kankane

3.Kankana

4. Kanana

5.Babba

6.Manya

To ga abin da na ke gani akansu:

1. Karami: Abu ne ko Dabba ko mutum wanda bai kai ga manya ba.Misali a cikin jimla. Karamin kane. Karamin Abu da sauransu.

2. Kankane: Ya fi zowa wajen baiyana mamaki.bai kai ga karami ba. Wato dan mitsitse kenan. Misalinsa a jimla.Wannan dan kankanen abu ne ma?

3. Kankana: Wato kanana fiye da daya. Misali kankakanan duwatsu.

4.Kanana: Jimlar karami ne. Misali. Kananan yara.

5. Babba: Bahaushe ke cewa "Babba ba yaro ba" Wato mai girma fiye da karami. Misali komai na Babba ya fi na yaro.

6. Manya: Jimillar Babba kenan. Misali. Manyan mutane,Manyan Kasunne da sauransu.

Ina jiran gyara ko korafi
Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124