Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 2 | 1009M26
....... A SHE BA KASAR HAUSA DAI A KE TASHEBA......

Yanzu daya daga cikin yaran da ke karatu wuri na Nafi,u Bello ke rera wata wakar tashe da harshen zabarmance. Tambayar da na yi masa akan ta. Game da bayan watan AZUMI ya kwana nawa su ke fara tashe? Sai ya ce da ni" Azumi da kwana shabiyar ake farawa akare tare da AZUMIN. Waton tun sha biyar ga wata sai ran daren sallah karama. Sannan a kuma shiga harkokin bikin sallah a wannan ranar har safe. Suna buga Nuk,awut kamar yada anka yi shekaran jiya daya ga watan daya" Ga wakar da ya dan reramin:

TABAI TABAI=AMSHI. TABAYE

GA DODO, TABAYE.

DA FU KWAI GIRBI,TABAYE.

WAKAR GA TUNADI,TABAYE.

.,.............. Kadan kenan daga cikin wakar ko da ya ke Anas Aminu da Sama,ila umar sunce akwai su da yawa ba wannan daya bace kawai.

Da na tamnaye su shin mata na yi? Sai sunka ce a a mata ba su yi.Don jin tabakin su matan sai na tambayi Malika Umar jinju ta ce lallai ita nata wayo bata taba ganin mata na tashe ba.

Ga al,adar kasar Sakkwato da kebbi da zamfara na san galibi ba a faye wuce kwana biyar ba. Ana tashe.

ABIN KULA

Idan kalli tsarin shirin masu tashe a Yamai za ka ga daya ne da namu. Rawa da sarholiya da nishadin daya ne.Gudun muwar da suke ba al,ada ma daya ne. Bambanci kawai shi ne yare zabar manci sunka fi amfani da shi. Don galibi ya fi yawa.

Yaran sun shaida min suna samun kudin yar lalurarsu ta Sallah da kuma dabno da Alewa da sauran abubuwa.

Da na tambaye su yaya su ke saka ka ya? Sai kowansu ya ta fi ya yo shiri kamar yadda ka gani a wannan hoton Nafi,u Bello Sakkwato a dama, Sama,ila junji a tsakiya, Jikan MH a hagu (Anas Aminu) Kamba.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124