Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 2 | 1009M33
..........KIRARI DA MA,ANARSA............

KIRARI: Wa su kalamai ne masu tada Wanda ake wa,har ya ji komai ya na iya yi,ko kodawa. waton washi ne da akewa mutum ya ji dadi ko ya harzuka har ya yi wani abin ban mamaki.

.......ire-iren kirari......

kirari ya kasu iri-iri.Amma ga biyu daga ciki:

1. Kira na washi: Wannann nau,in kirari ne da akewa mutum,Wanda Galibi maroka ke yinsa. suta zuga gwaninsu su na fadin ayukansa na alhairi da ayukan da kakanninsa da iyayensa sunka yi. Saboda jin dadi,shi Ku ma yaba su kyauta ta azo a gani. wannan an fi wa saraki da yan siyasa da wasu manyan mutane.Misali. kirarin saraki: Dan sarki jikan sarki, Allah ya sa ka gadi ubanka, kamar yada ya gadi ubansa.sarauta dole, in babuku gari ya watse........

2. Kirari a cikin waka: Shi kuma wannan nau,in kirarin yan tauri da yan Dambe ne ke yinsa. misali.kirarin Hamza Dan Alhaji inda makidinsa kalla ke masa waka. Alokacin da anka gayya ce su a RIMA REDIYO SAKKWATO.

"Bissimillahi ya Allah,Ya karimullahi,Ya sarkin dare da Rana Allah,Ka taimakan ga wagga Sana,a,don Dahe,don Kala,don innamasabilu saurara min ka ji maganar uban su a,I baban sallama,kan-karar ta ma na Alhji mamman,ba noma na mu Kai ba,ba karatuna ba,balle kace ka sa min kuiya,koko kace kasa min sura. AI wallahi ko karatu na mu ka yi,In ka ja baki inai ma hwassara,ni a uban su a,I wake-waken Malam rabi kahiri,rabi musulmin Allah. in ban da kahircewa mikasa musulmi kumya,ml ka sa musulmi kuwa. Kalla Mai kidin kasaken arna? Ka hwada min diya maza wadanda ka yi ma waka,wadanda Anna garinku,KO wadanda Anna kasarku,in hwada ma maza wadanda na buga da danyat geza, anan Dan tasakko birnin daji, na tiki Bako na bugi Araga na yi ma Dan Kaduna hudin Bota,saura Hamza Uban yat Abu, bagudun gwaddodi,duk Randa munka hade da shi wuta na ci nai,sannan mu ka zarkade Duniya mu Mai sad danya,malaminda ya (gamtse) matar da nai, karika mu ka ma dungululun aiki..

........"


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124