Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M36
===== BUDADDIYAR WASIKAR TAMBIHI======

Wannan wasika za ta dan tsakuro bayani da tunatarwa ga musulmi.

Ka zama mai hakuri,don hakuri turbar nasara ne.

Ka iya harshenka,don shi ne zakinka

Ka kasan ce mai yi ma kowa kyakkyan zato, saboda kaima a yi ma.

Ka yi ma kanka hukunci,kafin Allah ya yi ma.

Ka zama mai girmama mutane,don ka samu albarkarsu.

Ka rinka ya fe laifi,don Allah ya ya fe maka.

Ka fita daga duniya,jama,a su so ka,Allah ya soka.

Ka zama mai gaskiya da rikonta,don ka tsira da mutumcinka.

Ka tausawa mai karamin karfi,shi ko Allah za ya tausaya ma.

Ko mai za ka yi ka lisafa.don kada ka rufta halaka.

Ka rinka ziyartar assibiti,don ka kara imani.

Ka rinka sadaka don kariyar bala,i

Ka lizimci sallar jam,i, don ka samu ribar da ta fi ka yi kai ka dai.

Ka yi abokai na gari,don ka zama na gari.

Kada ka dauki jita-jita,saboda kuskure ne.

Ka zama mai rike amana,saboda cinta bala,i ne.

Ka da ka zama cima kwance,saboda wata rana gori za a yi ma.

In ba ka san abuba,anka tambaye ka, kace ba ka sani ba.

Ka rinka sadaka don kariyar rubushi.

Abin kwarai ba a boye sa,sai dai mugu.

Karinka wa malammanka da iyayenka da musulmi addu,a.

Ka dai na zagin shuwagabanni,addu,a ake yi ya fi.

Ka dai na saka abu a ranka,yin haka yana taba lafiyarka.

Kasan duk abin da ka ke,ana rubutawa.

Kada ka ci amana,musamman ta karamin yaro.

Ka yi soyyayyar Aure,bata batanci ba.

Ka zama mai karanta al,kur,ani, don samun alhairan da ke ciki.

Mu tsaya anan,za mu ci gaba.

Don Allah duk wanda abin cewa. a game da irin wannan ya yi.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124