Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 2 | 1009M43
====MUTUM-MUTUMI NE DAI-DAI==

MAKARANTAR HAUSA TA nemi bayanin wasu kalmomi ko ince sifofin da sunka jima su na bukinsu acikin nishadi a masayin tawaye.Wanda ta ke ganin daya yayi wa daya basaja ne. Ta nemi a baiya na wane ne dan basaja acikinsu.

Abin mamaki na ga su kansu kafafen sadarwa suna amfani da su. Duk a cikin basajar,musamman BBC HAUSA,don ko a shekaran jiya sunyi amfani da siffar BUTUM-BUTUMI,wata kiila ma shi ne dalilin da ya sa MH ta tsamo labarin. Don a tantance ma mutane Aya da tsakuwa.

To kuma a fanni daya MH ta baiyana cewar manyan kamus na Hausa sun yarda da su duka. To ni ma na yarda. Amma da daya wato mutum-mutumi.

Dalili na

Ka aje hankalinka ka kalli abin da kyau,in za ka lura zaka ga yayi kama da mutum,ta fannin sura. Bambanci ka wai shi ne rayuwa,tafiiya,tunani da sauransu. Don haka ko bai da ce a ce da shi Butum-Butumi ba. Sai dai a ce MUTUM-MUTUMI. Duk da juyawar kalmomi al,ada ce ta hausa. Amma wannan Juyawarsa ba haka ta ke ba. A dai sake nazari.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124