Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M44
======KAFIYA ASIRIN WAKA NA 1 ===

GABATARWA

Wannan dan rubutu za ya dan yi bayani akan wak@r hausa,amma kuma rubutatta. Don nuna muhimmancin amfani da kafiya da tsarin yada ya kamata a shirya baiti.

Don ganin yada galibin matasa sunka fi maida hankali ga waka. Ta soyayya ko bege ko siyasa ko nishadi.yasa naga aini ma ina da filin cewa wani abu. A wannan farfajiyar.

Ko da ya ke ni kaina ina cikin wadannan matasan a da. Don in zan iya tunawa a shekara ta 2013 na taba wakokin. Inda na samu damar fitar da guda biyu kacal. Daya ta Auren yayan aboki na ce. Wadda ISAH ALIYU ya yi ma yan gyare-gyare. Na yi wannan wakar a SIrajo sound r.....wanda a yanzu haka cdinta in ba ya salwanta ba yana hannun Kasimu Bello.Ko ince a hannun makarantar hausa.Wakar maitaken:

Kowa ya cashe babu canki-canka,

Ridwanu anga shida Basira yau sunyi aure.

Sai ta mahaifiya ta da na yi alokacin da ta yi wani rashin lafiya mai tsanani. Na sa ma wakar Cuta ba mutuwa ba. Ga amshinta:

Cuta ba matuwa ba,

sharan kwalla ummina.

Ita ma a sirajon anka kida ta, kuma Nakofa ne yayi kidin. Duk da ya ke ina da wakokin tari. Amma wani daga cikin mahaifa na,kuma jagoran karance-karance na ya ce in daina. Sai na taka burki anan. Ni dai bansan dalili ba. Amma dai na yarda da duk yadda anka yi ya hango wani abu da ban hango ba. To amma duk da haka ya ban yar tazara ta ina yi in ba wani ya rera. To Alhamdu lillahi,a gefin waka ina da yaran da na koya ma ita samaga goma. Kuma ba na shakkar su a fagenta. A kowanne fanni na waka. A kwai abokanin dake ta ambatar suna na da godiya a wannan fanni. Sai daga bayannan na hana a saka sunana a kowa ce waka. Abokanin sun hada da babban abokina,na hannun dama. Watau IBRAHIM MUHAMMED( I.B.GORA). Da zayyanu Dodoru( A LAUYE) A Kwai kuma wani dan ajin mu Faruku ALIYU,K. Sanyi(Ringine) wanda daga garesa ne na hana a saka sunana a waka. Na yi ma wata mata, gyaran wata waka,mai suna lover-lover, anan yamai za akai wata daya a yanzu.

Abinda na fahimta ga sauran wakokin zamani akwai matsalar kafiya a ciki. Don haka zan rika bayanin ta kadan-kadan dai-dai hali. Yanzu kuma ina ba makarantar da na kare G.D.S.S.MALISA hakuri don rashin gani na. Acan ma ina koyarda wannan maudu,in. A bara ma an samu wanda ya fitar da waka. Mai suna bankwana da yan uwa na. Na ji dadin yaron sosai. Bazan iya tuna sunan saba. Amma dai dan sabon Birni ne ta karamar hukumar mulkin Gwandu. Allah ya kara musu hazaka. Ba su san da MH ta fara aiki ba da yanzu sun garzayo. Da ya ke na ga daya yayi rijista kwana biyu da sunka wuce.

Don haka zan dan yi bayanai daki-daki da kuma misalai in Allah ya so. To amma daya ke ina kusa ga masu gidaje na da abokaina da ma iyaye na. Bahaushe ya ce" Dan dangi bai kunya" kuma mai uwa a gindin murhu ba zai ci tuwonsa ba miya ba. Don haka inda anka ga kure na sai a yi ta yi min gyara. Mai karami ne da babba in ya daure.

WAKA: Wani zance ne mai cike da hikima da fasaha,wanda ke zowa a dunkule.

A kwai ire-iren wakoki da da ma tun daga na gargajiya zuwa rubutaci. Wanda a wancan lotto ba kida ake da wakar ba. Sai dai a yi wakar a maidata littafe ko fai-fain garmaho da sauransu. Sannan wasu ma ba ka jinsu sai a gidan rediyo. Kamar RIMA RADIYO SAKKWATO da REDIYO TARRAYA KADUNA.Wadannan mawakan sunyi hubbasa sosai Allah ya saka musu da alhairi. Don gaba daya wakokinsu tunatarwa da nuni ne jigonsu. Kamar DR Aliyu Akilu Jegga,Na,ibi S. Wali,Alhaji mudi sipikin Abakar Ladan zariya, Malam Aliyu Na mangi zariya da ma wasu da dama da sunka taka rawar gani. Allah ya biya su. Duk wani mai yin waka a yanzu sawunsu ne ya ke bi. Ban hana gaurayen da a ke samu da turanci ba. Inda sukuma sunfi saka larabci a cikin wakokinsu.

Mu dan tsaya anan, sai mun hadu a kashi na biyu.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124