Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M48
SANI YABO(S.S.YABO)= KO KA MANTA?

A cikin biyayya da girmamawa da kyautata zato ga mai Gida sama,ila S.S. YABO, bakinmu da tunanin kwalwarmu da wani barayin jikinmu. Suna cike da mamaki da alhini da sanin yaya za a yi. Ko yaya anka yi? Ko ban ce komai ba mai gida sai na ce kana da laifi. Sai dai ka gafarce ni. Ni a nawa gani wallahi ka manta da MH ta na bukatar taimakonka.

Mai gida ka duba fa dukka nin takwarorinka sun dan ce wani abu mai yawa da muhimmanci da ilmantarwa. Wa su sun dora shafuka,wasu littafai sunka daura,wasu waiwaye sunka yi akan rubuce-rubucen MH. Wasu tambihi, wasu shawarwari. Amma mai gida ko ka manta da MH ta fara aiki. Tun lokacin da ka yi rubutun maraba da MH ba ka kara cewa kule ba ballai cas. Shin mai gida ba ka ganin wannan a matsayin kuskure da ko in kula ne ka yi? Ya kamata duk aikin da ka ke matsuwar lafiya ka ke, karinka taimakama MH da rubutunka. Hatta ma da litta fenka mai Gida ya kamata a ce ya hau wannan wurin. Wallahi ka na da nauyin da Allah ya dora ma na MH fiye da sauran mutane. Kuma in ba ka sauke sa ba,ka na iya haduwa da fushin Allah. Mu ma fita maganar MH mu koma ga hadisin da na san ka sanshi." Duk wanda ya boye sani, ranar kiyama zaya tashi makaho" Ko kadan ba na son abin da ya sa haka a gunka. Allah ya dora ma nauyin MH don Allah ka yi wani abu mai gida. Sai da taimakonku ne fa nasibin MH za ya kara bunkasa. Don ku ke da hanyoyin karta kwana. Ina da yakinin wallahi daga dawowarMH zuwa a yau,ka yi rubutu koda daya ne a wata kafar sadarwa. Me ye laifin MH da ita ba ka yi mata ba ? Ya mai gida. Ko ka manta ne? yi hakuri, in abin ya bakanta ma. Yaronka,mai biyayya da tunatar da kai, da fa ka ce "ka na yi ma laifi bai taba magana ba" in zaka tuna C.O.E sokoto. Nasan za ka tuna.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124