Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 2 | 1009M52
====ZUWA GA SAMA,ILA SANI YABO=== KO YA MANTA?

A bisa ladabi da biyayya da kira a barayi daya na gangar jiki da tunanin shin lafiya. Barkwanci da girmamawar da babu raini. Hadi da hubbasarsar baiyana tuna tarwa. In an manta.

Bayan kwashe kwana dakwanaki da fara aikin MH. Tun da S.S.YABO ya leko ya koma,kuma sai ya yi batan dabo. A cikin kogin bahar maliyan da mu ba mu sansa ba. Mai gida in an kamo kihi da kada,kuma kar a manta ina bukatar fatar giwar ruwa. Don ina son in danyi wani abu da ita.

Mai gida wata majiya ta ce wai don aure yayi dadi ne, a yanzu ko rubutu su amartu ba su bari kayi? To in haka ne Allah ya kara bada zama lafiya. Amma fa a gayawa uwar gidan mai gida na. Ta dan ja masa kunnen nan na soyaiya. Ta gaya masa kamar haka: Ango na,uban yayana, mai kwantar da hankali na, wanda na ke son rayuwa da shi mai dorewa. Wani yaronka da na ke jin an ce kunshaku da shi ne ya ce. Ko lafiya an rike ka an hana maka rubutu musamman a MH?

Mu fa yanzu mu na tunanin aure ne ya hana mai gida ko da rika al,kalami. Amma dai mai gida ko baka yi rubutu a ko ina ba MH kan ya kamata a ce ka dan a za mata littafenka na YAR HALAK don takwarorinka duk suna nan suna ta kara kaina abisa siradin kyautata adabi da al,ada. Donko bayan ka yi ta leko ta koma. Su da sunka leko ba su koma ba. Ni fa ina gaya ma MALAM. Kai ! mai gidan nan nawa ko. ko ya bar alkaaminsa kan katifar makeken Gadon amartu? Sannan banga takardar rubutunsa ba a MH , Ance ta na can kan danin table. To mai gida a fada ma anty ta ta dan sako mana kai. Don fa MH ta kosa da rashin ganinka. Anty ki fada masa. Da ya timaki mai son tashi, ya taimaki wanda ke son taimako. MH ce ta ce taga a cikin shafinta batagansa ba. Ballai ya ya dan zuba mata wani abu a cikin rumbunta, na shafi. Shi ma sashe daya na ta wato magama ya fashe min da kuka, wai tunda mai gida ya yi mai sallama bai karaso a falonsa ba. sai ya rego cikin gida dai ya koma. Hulda ma cewa ta yi su mai gida ko an manta. Shi kuma amsa'amo ya ce oho! Ku ta shafa. Wanda tun da yazo ko duriyarsa ba a kara jiba. Sai na ba su hankuri da cewa Abu Hidaya fa ya shigo kuma ko sun manta da DAN SIDI MANANAN? Sai magama ta ce da ni kama bakinka. Yaro in ana babbakar Giwa wa za ya ji kaurin Bera. Ana magana da manya,kana kado bakinka? Ni ko kasan baki na bai haila,ballai najasa ta kamasa ya daina sallah. Sai na amsa da sassaukar muryar girmamawa. Na ce to don ina kara mi, me na yi kuma? Bayan ina danyin yan zane -zane na. Ko da duk yada suke ai mai karami babba za ya damka inya gane. Sai ta ce "shin A.D GORA ne? Na amsa eh. To yi hakuri,Babban mai gidanka SS ne ya yi mana ta leko,ta koma.Sai na kada baki na ce ma jagorar su wato magama. Halan ni ma baki ga ina ba MALAM cigiyarsu ba? Sa i magama ta ce anyi haka.

To mai gida wallahi baka kyauta ba da ka kyale makarantar hausa haka. Ka na cikin yan karta kwana ,don haka kunfi kowa hanyar taimakonta.Yaronka A.D.GORA KE BAKA HAKURI.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124