Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M53
=========IRE-IREN CAMFI===
Na ga MAKARANTAR HAUSA ta dan tsakuro ma,anar CAMFI da misalansa.
Amma kuma kamar naga bayanin a dunkule ya ke. Ya ko da ce a ce an dan buda shi.
=== GA DAN NAWA KARIN===
BUNZA A.M.(2006) Ya kawo ire-iren CAMFI, kuma galibin su duk na yi nazarinsu. Kuma naga lallai yada yayi bayani haka ne.
Ga kadan da zan danbayar a cikin wadanda ya bayar.A kwai na Aje abu.kamr yada MH ta danyi bayani. Ga wasu:
A- Camfin lokaci
B-Camfin rana
C-Camfin Tafiya
D- Camfin zama
E- Camfin cin abinci
F-Canfin Aje Abu. Da sauransu.
Bari magansu da misalansu
Camfin lokaci: wannan camfin akan lokaci ya ke magana. Misali.ba,abarin karamin yaro bakin garka da mangari ba. Wai in an barshi ya na iya gamo da iskoki.
Ba a tafiya daji darana tsaka. In anyi shima ana iya gamo
B-Camfin rana: Wannan camfin shi kuma akan rana hausawa sunka rataya shi. Misali ba,a tafiya ranar talata. In an yi da wuya a samo sa,a.Ds.
C- camfin tafiya: shko akan tafiya hausawa sunka mika shi. Misali. Ba a fita gida kusan sallar magariba. Ta na iya yiwa kan hanya a hadu da jinnu za su gida.D.s.
D- Camfin zama:wannan camfin akan zama HAUSAWA sunka daura sa. Misali. Ba a zama bakin dangarma. In an zauna Ragon kafa na ture mutum
D.s.
F-Camfin cin abinci: shi wai ba a cin abinci tsugunne. In ana ci zubewa ya ke a kasa,ba a koshi.
To kamar yada MAKARANTAR HAUSA TA CE, Dibara ce kawai ake yi don kauce ma wani abu. Wanda ake ganin yana iya kawo matsala ko ba a sonsa. Sai a kakaba mai camfi.
==== ABIN KULA===
Shi bahaushe ya dau camfi fa, kamar hadisinsa. Kusan kamar yada ya dau karen magana.