Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M54
=======DAN MH DA JIKAN MH A YAMAI,KE YIN MUKU BARKA DA JUMU,A====

Ga addu,armu:

Ya Allah ka ba mu zaman lafiya,

Ya Allah kara muna hakuri,

Ya Allah ka daukaka mu,

Ya Allah ka shiryar da mu,

Kashiryar da yaranmu,

Ka shirya muna manyanmu,

Ka shirya muna malammanmu,

Ka shirya muna iyayenmu,

Ka shirya muna sarakunanmu,

Ka shirya muna yan siyasarmu,

Ka shirya muna shugabanninmu,

Ka shirya muna kasarmu,

Ka shirya muna duniyarmu.

Allah ba mu da, ka ba mu

Allah ka kyautata jiya,da yau da gobenmu.

Allah ka jikan musulmin da ya rasu da wanda ke raye.

Ka daukaka makarantar Hausa da Ahlinta. Ka kara ma iditanta lafiya da kuzari da hakuri da bin hanyarka.Allah ka kyautata bayansa,ka kyautata yau dinsa,ka kyautata gobensa. Ka taimaki duk ahalinsa da mai sonsa. Ka shiga tsaninsa da makiyinka (shaidan). Ka daukaka dukkanin a yukansa da na duk memban MH.

Don haruffan da ke cikin Qur,aninka,

Don Ayoyin da ke cikin Qur,ani,

Don surorin da ke cikin Qur,ani,

Don Qur,ani mai girma.

Ya Allah don hallitunka, nakasa da sama tudu da na ruwa.

Allah don Annabawanka,tun daga Annabi Adam har zuwa ga Annabi muhammadu (S.A.W).Don bayinka wadanda sunka bika tun farkon duniya har karshenta. Amin!Amin!!Amin!!!

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124