Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 2 | 1009M60
====ISKOKI====

GABATARWA

ISKOKI dai halittu ne da Allah ya yi,kuma ya boye su daga ganinmu, mu yan Adam. Amma sauran dabbobi na ganinsu. Haka kuma suna hawan kansu,su juya musu tunani. Kamar yadda su ke juya mutum a wani lokacin.

Iskoki galibi suna hawan kan dabbobi kamar kosashen sa da mazuru da gada da barewa da zaki da sauran dabbobi,irinsu kadangare da tsari da bushiya da sauransu.

A haujin mutane kowa sunfi hawan kan mata. Bunza A.M(2006)L .Y.Mai gidan sama (20018)"ISKOKI na hawan kan mata ko aurensu don ganin kyawonsu. Saboda su matansu basu da kyau,irin wadannan matan aka ce ma masu mazan dare. Haka matansu na aurar maza daga cikin yan adam sai kaga mutum ya kai munzalin jika. Amma babu ko aure. Saboda bai shawar ya macce"

Mene ne iska?

Iska boyayyen sunan hausawa ne da sunka ba aljani.Ga sunayen da Hausawa sunka ba Aljanania sakaye:

Iska: don yana shiga cikin abu ya fita,kamar yada iska ke shiga.

Mutanen boye: Dn suna a boye,muka ganinsu basu ganin mu.

KWANKWAMMAI: Saboda suna shiga kwalwar mutum da dabba.

MASU ABU: Saboda suna damar dauke komai na mutum"kadan kenan daga cikin sunayen da Hausawa ke kiran iskoki da su.

Haka kamar yada muke kashi-kashi da kuma tsarin rayuwarmu suma haka suke. Siyasarsu garuruwansu da ciniaiyarsu da zamantakewarsu da tamu babu ban-banci Duk suna yi. kamar yada manazrta suna yi ta baiyanawa.

KABILUNSU

A.M BUNZA,L.Y Mai gidan sama,B.B.Magaji duk sun baiyana cewa iskoki suna da Kabilu,kamar yada mutane suke.kamar haka:

Turawa

Larabawa

Adarawa

Fulani

Hausawa ds.

Bunza, "kada ka yi mamakin aljani ya haukan Bahaushe kaji baya hausa ko yana turanci ko wani yare, ka yi mamaki.Yadda abin ya ke idan ya kasance can wurin da anka daukosa wannan yaren ne kawai ya iya to shi ne zaya rinka yi.Saboda yawace-yawacen yan Adam. Kuma galibi su iskoki suna sunke ne ga yan adam.Don haka duk yaren da kaji suna yi wasu shi kadai sunka iya. Wasu kowa shegantaka ce da rainin wayo"

BABBAN BIRNIN ALJANNU

Masu nazari sun yi hasashen babban birnin Aljannu na duniya yana kasar Gobir,watau KWANKWAMBILO wasu kuma sunka ce a kasar Argungu ya ke ta jahar kebbi. To ni dai nawa hasashe ya zama daya da na Bunza, wato A jahar sakkwato. Dalili na kowa shi ne aduk lokacin Noman farko ina jin kide kide suna fitowa daga can yankin. Na tambayi wani tsoho sai ya ce dani" Tun suna yara su ke jin wannan kdan" abin da zaya baka mamaki wasu samari suna ce sai sun zo wurin. Sunka kama tahiya har sunka gaji amma sai kara jin kidin suke yi gaba.

Bunza ya duba A yankin Argungu Kuma ni ma nazo can a lokacin da nazo inda Bagayi na kwalejin ilimi ta Adamu Augi da ke garin Argungu na kara fahimtar wani abu akan maganar Malam A.M.Bunza na cewa" A kwai manyan duwatsu da koguna da Tsaunuka da Rafuka a yankin don haka hasashe ke nuna can ne Jangaran ya ke. Kutuna fa ba BORIN da ake kira Jangaranba. A,a birnin aljannune.

ASALIN SUNAN ALJANNU

BUNZA,L.Y.Mai gidan sama, sun kawo sunan asalin sunan Aljannu kamar haka:

Aljani: daga kalmar Aljannu ta larabci.

Jinnu daga kalmar Jinnu ta larabci.

Iblishi :daga kalmar Iblis uban Aljannu.

Rauhani: Sunan da ma a bota tsibbo ke masa.

Ira,izai: sunan ya samo asali daga larabci.

IRE-IREN ALJANNU

ALJANNU sun kasu gida biyu kamar haka:

1.Farfarun Aljannu basu cutarwa.

Babbaku Aljannu:Su ke cutar da dan adam.

SUNAYEN ALJANNU ATAKAICE

Malam alhaji:baya cutarwa.

Tsurut-tsurut:Ubansu kenan dan karami ne bai kai dan tsatsumbe ba.

Dan tsatsumbe: Dan karami ne kuma mugun takadari da son mugun wasa. Ya fi fita da rana tsaka.

Gum-gumgum

Doguwa: Baka ce da gashi har kasa ita baka gashin haka.

Jitakuku.

Inna: ita ce uwar aljannu. Kuma ita ke tura yayanta ga mugun aiki.ds.

WURIN ZAMAN ALJANNU

Galibin wurin zamansu shi ne cikin kogon kuka ko tsamiya.

Saman bola

Ban daki

Kangon gida

Kan wasu dabbobi

Cikin ruwa

Bakin kofa

Kan hako da sauransu.

Lokacin fitar Aljanu

Da rana tsaka

Tsakiyar dare ds.

Lokacin komawarsu

Kusan magariba

Kusan asuba

Abincin Aljannu

Idan za su kasuwa suna saka tufafin saki da malfa da rufaffin takalmi. Basu yawan magana. Abin da sunka fi saye shi ne

Tsamiya: kunu suke da ita

Taba wiwi: shiya sa ma a ke ce mata tabar aljannu. Sunfi mutum shanta. Kuma ka tambayi mashayi,aljani ya taba bashi tsoro. Za ya amsa ma da a,a.

Taba sigari: kwali ko fiye suke saya.

Kanwa.

Turare: sha suke.

kambalawa

Ina gode ma Allah da ya ba ni damar kambala wannan dan abin da na gutsuro don baiyana shi ga MH da mu sauran dalibban nazari.

Godiya ga

Farfessa ALIYU MUHAMMED BUNZA

DA Malam Bagayi na kwalejin ilmi ta Adamu Augi Argungu da Lawi Yusif mai Gidan sama da injiniya Baba magaji da Malam Muktari Sahabi GORA da A.B. SANYINNA da Dakta usman B sani. Da Yusif ladan sanyinna da gamin gambizar malammai na da masu gidajena. Wanda da bazarsu na ke taka rawa musamman Sharfaddeni Umar Dogon daji leadership Haisa da N.B.Babi da S.S YABO d Isa Rasco Dangoma. Da uwat kuma ubana MALAM BELLO DAN YAYA,IDITAN MAKARANTAR HAUSA. Ba don sa ba da A.D.GORA baisan menene alkalami ba ko wani rubutu. Na gode. Na gode Allah ya biyaku. Ya sada mu da lhairi.Alhamdulillahi rabbil alamen

Inda gyara ya ke don Allah ina jira ga kowa ne.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124