Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 2 | 1009M64


======MAITA===

MAITA:kalmar Hausa ce da Hausawa ke amfani da ita don cika wasu muradun su na tsafi. Ko in ce aiki ne da suke yi don cimma muradin rayuwarsu ta hanyar amfani da iskoki da tsafe-tsafe da bakar tambaya da ganin kyashi da gunewa.

Maita ta kasu gida- gida. Ga wasu daga ciki:

A- maita don tara hatsi.

B-Maita don neman suna.

c-maita don jarunta.

E- Maita don buwaya.

F-Maita don keta

G-maita don neman kudi. Ds.

Wadannan su ne kadan daga cikin kashen-kashen maita. ko mu ce nau,ukanta.

=====DALILIN ZAMA MAYE===

A kwai dalilai da dama da kesa mutum ya zama maye kamar yadda Malam Aliyu Bunza ya fada. Mutum na iya zama maye ta hanyoyi kamar haka:

1-Yawan cin itacen tauri ko wani Asiri.

2- Hadiyar kankarar maita.

3-Gado ga uwa ko uba.

4--Cin wainar maita(wata majiya)

Da sauransu.

=====ALAMOMIN MAITA===

MALAM YA kawo alamomin maita guda bakwai. Kamar haka:

A- Jan ido

B-Kadaici

C-Yawan girki

D-Bakin rai

E-Rawa

F-Rashin Bacci

G-Bakin Nufi.

ina tunanin ba su kadai ba ne. Da ya ke littafan duk basu a hannu na a yanzu. Abin da ke gare ni ne a ka, na ke bada misali da shi. Da kuma sauran wadanda na dan bincika ta yanar Gizo. Saboda nisan da na danyi da kayan karantu na.

==== BAN-BANCIN MAITAR MACCE DA TA NAMIJI==

=====[Maitar macce===]

Ko tantama babu duk abin da macce tasa kanta na fannin shirka da tsafi da ridda da bakar bida,sai ta fi namiji shahara ga wannan abin. Shi ya sa macce maiya tafi namiji bala,i,.Sau tari maiya ke kamu taki saki. Sai dai a mutu. To shi ko wanda ya sha Nonon maita, shi ne sha kundun. Idan na ce wanda ya sha Nonon maita,ina nufin wanda mahaifiyarsa maiya ce, sai kuma ya sha a Nono. Shi ya fi ma mahaifiyar bala,i.

=======Maitar Namiji===

Shi namiji ya na da yar dama. Saboda dawuya ka iske namiji da maita ba ta dauka ba ce. Kuma ta dauka na iya zama don neman kudi,dukiya,hatsi,ds. To in ka duba za ka ga abin na motsawa ne.

====Yaya maiyu ke rawa====?

Lallai wannan tambayar na da kyau. To maiyu su na rawa a cikin dare. Musamman a lokacin bazara. A lokacin da su ke wannan rawar ance, ba duk dan nisa ne ke sa basu ganinka ba. Da kuma makamin da ka dauko ba. Su na da sauri kamar walkiya. Kuma ance in za su yi wannan rawar sai sun fitar da fatar jikinsu( Ban sani ba). Bunza ya yi magana akan lokacin da su ke dawowa daga wannan rawar."Duk wanda sunka gamu da shi a wannam sa,a to ba da shi ba".

=== Yaya maye ke kama kuruwa====?

To wasu sunce maye na kama kuruwar mutum ta hanyar

1. Yin musabaha da shi.

2.Takin inuwarsa(wata majiya)

3.Kama kuruwa(Babu tabbas)ds.

==== Yaya ya ke da ita====?

Idan maye ya kama mutum ko kuruwarsa. In mun yarda da kuruwar,an ce zaya kaita a:

Ko a kogo

Ko ya daga dutse ya binne.

Ko ya saka a cikin kwalba ko wani wurin da bata iya fita.

Da yawa za ka ga mutum ya na da kamun maye,amma sai dai suta wahalar da shi. To irin wannam an yi-anyi yaki ciyuwa. Don haka sai a barshi nan haka nan. Sai rai ya yi halinsa. Ya yi ta wahala.

=====Me nene maganin maye===?

A kwai dai mayen maiyu,wanda shi ko maiyu yake kamu. Akwai ita ce dari ba daya 99. Da ake amfani da su. A kwai kuma masu bada magani, a sha a warke. A kwai masu bada magani, sai a ji wanda anka kama na fadin. "wane me na yi ma"? Ko wance ki rabuda ni.

Idan mutam ya buyawe wanda ya ka ma shi, sai ya kaima uban gidansa.

===BABBAN RASHIN ADALCIN MAYE=====

Kowa baya ragama,dansa,yarsa,matarsa,kaninsa,abokinsa,ballai dan uwa da abokan arziki da yara da matasa. Su kamar bayi ne.

Maye ko ya kama anka je assibiti aikin banza ne. Saboda babu wata na,ura da ke iya gano kamun maye,a yanzu dai kan. In ka je kotu ka wahalar da Alkalai. Don ni wannan ta faru gaba na a Kotun Gwandu da ke jahar Kebbi. Wani yaro ne, wani tsoho a ke zargin shi tsohon ya kama yaron. Shi ne iyayen yaron sunka kai wanda su ke zargin. Sai ya ce,shi kazahi ne anka yi masa. A gaba na dai ya na bisa hanyar cin nasara. Saboda babu wata hujja mai karfi da ta baiyana Shi ya yi kamun. A.m.Bunza "ya ce irin wannan shari,ar ta taba cin wani alkali" To abin ya na da daure kai. Da ban al,ajabi a shanin maita. Saboda tsafin da ko na,ura bata iya gano komai a sha,anin.

Shawarata kawai, duk kotu ta tanadi mayen-maiyu daya ta aje. Ko da gudun muhawara.

To daga karshe ku sani jama,a a musulunci kandun baka anka sani. Ba maita ba. Don haka maita tsafi ne kawai da ake hadawa da aljannu da cin ita ce da yawa da gado ke kawo ta.

Wannan dan bayanin ina dunkule shi ne sosai da soai. Abi sa ga yada ya ke cikin littafen.

MAUDU,INMU NA GA BA SHI NE KANBUM BAKA.

GAISUWA GA

FARFESSA ALIYU MUHAMMED BUNZA.

MALAM BAGAYI KWALEJIN ILMI TA ADAMU AUGI ARGUNGU.

MALAM MUKTAR SAHABI GORA.

NASIRU ABUBAKAR(Matawalle) na aromin littafen GODON FEDI AL,ADA da yay min.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124