Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M65
==A SHE RASHIN MASOYI NA SA RASA RAI===

A jiya wani aboki na Dan Zariya,ke ba ni wani mamaki game da labarin soyayyar kakanninsa guda biyu.

Ahmad ya tabbatar min da cewa wannan labarin wallahi da gaske ne. A kan haka ma idan ya na son shammatar kanin Babbansa ya na tsakure da wannan labarin. Da ya ke kanin Babban na sa mutum ne mai son nishadi.

==== Soyayyar wasu tsofafi biyu A Zariya===

Wasu tsafafi ne guda biyu, sun taso tun suna yara . Su na ta sharar soyayyarsu,har sunka yi Aure da yaya da jikoki da dama.

Alla mai hadawa, kuma mai rabawa. Kwatsam sai mijin ya kamu da rashin lafiya. A she ciwon shi ne ajalinsa. Bayan ya rasu, matar tasa sai sharar kuka ta ke. Kowa yana zaton irin kukan nan ne na dan jimami. A na ta tausarta da ba ta hakuri. Sai ta ke cewa." A rabu da ita fa, ita ma lokacinta ya yi ne". Ana ganin maganar wasa-wasa. Ai sai sharar kuka ta ke. Yanzu wane ya tafi ya barni? Ahmed na ba ni labari. Ya ce" Wallahi bata kwana ba. Ita ma ta bi mijin.

Na manta ban tambayi Ahmed sunansu ba. Amma zan bincike sa da yardar Allah.

Ya Allah ka jikan masoyanka,ka jikan wadannan masoyan. Ka hada su a Aljannarka. Kyautata bayansu. Ka ba mu matan da za mu rayuwa kamar tasu.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124