Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M67
===FATALWA===

Gabatarwa

Masana da masu bincike sun ta kirdado akan FATALWA,wasu sun bada ra,ayin babuta, a gefe daya kuma sun bada akwaita. Idan zan iya tunawa sashen HAUSA na BBC ya taba tattaunawa da wani Dr na jami,ar Kano,wato Jami,ar Bayaro Kano.masanin anasa bayani babu fatalwa.

Sai wani bincike da wasu gamin gambizar masu ilmin fasaha. A karkashin jagorancin DR.Giulio Rognini na cibiyar fasaha ta Swizaland. Sunyi gwadi ga mutum 10 da sunka ce suna jin motsin abu a wajen da suke. To kuma Dr ta ya gayawa BBC da cewa"Wannan abu ne da a ke ganinsa a zahiri". Bayan kuma an sake gwada wasu masu hankali guda 40.Ba,a same su da wannan ba,to duka dai bayanin yana magana akan fatalwa ne.

In babu rami miya kawo maganarsa?

L.Y mai gidan sama (2017) ma ya ce wani abu a cikin GADON FEDE AL,ADA,amma atakaice.

=== Bari mujita daga Bakin mai ita Farfessa A.M BUNZA(2OO6).

Shi kansa farfessa ya yi hira da Bbc a kan wannan. Amma yanzu bahirar zamu bi ba. Littafen za mu bi. Gwargwadon hali da abinda anka fahimta.

Mene ne FATALWA?

Wasu kasusawa ne da ke da diri kamar na mutum ko in ce maka na mutum din.Wadan da bayan mutum ya mutu ko ankashe shi ta wasu hanyoyi ya ke canza kama. Ya koma kassa zalla ya na bibiyar mutane,galibi a cikin dare.

Za ka ga kasusuwan mutum ne,amma babu nama da fata. Kuma baya magana.

==Dalilin zama fatalwa==

Bunza,A.M,(2006) Ya nuna dalilan da ke sa mutum ya zama fatalwa. Shi ma L.Y. Mai gidan sama yabi layin Bunza, Ga dalilan da sunka bayar.

1.lokaci: Idan mutum na cikin lokacinsa,Sai anka kashe shi. Ya na iya dawowa ya ida lokacinsa. Musamman ma matashi.

2.Kiyayya: wanda anka nuna ma kiyayyar da har ta kai shi ga rasa ransa na iya zama fatalwa don ya dau fansa.

3.Soyayya: So na sa mutum ya zama fatalwa ya rinka bibiyar masoyinsa. A matsayin mai karesa.Ita fatalwar kare masoyin ta ke. Shiko ganin ya ke kamar halakasa ne za ta yi. Idan masoyin yayo dare daga wani wuri,ya biyo ta sashen da Abokinsa ke ruhi a makabarta. Ya na iya zama fatalwa yayo masa rakiya. Za ka ga mutum yadda kasan tsayinsa. Amma babu nama,, sai kassa da jijiyoyi..Haka zaya rakayo masoyin sai ya shiga gida shi ko ya koma.

4.Guri: Idan mutum ya mutu da guri,yana iiya zama fatalwa. Yadawo don ya cika gurinsa.kamar daukar fansa.Ds.

5.Waibuwa: wannan a fannin saraki da manyan mayaka da wasu manyan mutane sunkafi yin wannan fatalwar.Misali sarki ya rasu,sai a ki ba dansa sarauta. To wannan sarkin da ya rasu n@ iya zama fatalwa ya hana ma wannan sabon sarki kwanciyar hankali. Ai shi ya sa kaga wasu sarakuna basu shiga gidan sarauta alokacin da anka nada su. Ni na san gari biyu a jahar sakkwato da ba su da mai gari ko sarki. Daya karamar humar mulkin shuni. Daya a karamar humar mulkin Tambuwal.

Mai son karin bayani ya nemi GADON FEDE AL,ADA na A.M.BUNZA. Wannan duk abin da anka gani a dunkule a ke aza shi. Amma acikin littafen an fadada abubuwan fiye da wannan..


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124