Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M76
====BARKA MAKARANTAR HAUSA DA DAWOWAR S.S. YABO===

A gaskiya yau INA cike da farin ciki da jin dadin da sai dai ince"ince Alhamdu lillahi. Saboda na wayi gari na ga Allah ya karba min roko na.

Dawowar mai Gida na da ga Inda ya je. Mun yi jimamin rashin cewarsa uffan na Dan wani lotto. A bin da ya kawo kuka garan da bakin ciki. Wanda ba ni Kadai ba ne a cikin wadanda wannan Ambaliyar tafiya da tunani ta rutsa da su ba. Hadda ubanmu,kuma uban tafiyarmu MALAM BELLO MUHAMMED DANYAYA. To ba a ganin laifin uba idan ya nuna bakin cikin rashin ganin Babban dansa a cikin wani babban aikin all,herin da ya yi. Musamman idan shi mahaifin ya duba a gefe daya, yaga kannen yayan suna cikin aikin tukuru.

KA SHARE MU NA KUKANMU

A gaskiya sama,Ila ka sharema Mh kukanta da duk mai kwarar hawaye akai. Musamman yada ka dawo da karfin da kowa dole ne ya ji dadi. Ni dai na fi kowa,sannan malam da sauran mutane.

Bari in ari bakin Mh in Dan yi kirarari ga s.s amma da bakin ta

A gaida mai hubasa,

Mai niyar bunkasa,

A yukan da ankasa,

Gaba don cusa,

Adabi da visa,

Kan all,adar Hausa,

Hadi da kinayar mafasa,

Nahawu da binsa,

Karta ta kwana a fannin Sanin sasansa.

A gaida da sani yabo,

Kada fa kuda mu,

A kan yabo ya samu

Gado tun masu samun,

Wato gari da iyayensu,

Ga shi dalibin masu kushisu,

Gado ga Mh an basu,

Sanin ya kamata ya sansu,

Biyayya da tarbiya an sansu,

Rubutu da gaskiya ai ba ya su,

Shi ne mai Dan Sidi a fanninsu,

Ga na Ta,ala duk layinsu,

Sannu mai nura Bello ba ya Ku,

Malamman kwaleji sun sansu,

Jami,un ilmi kan sun ba su,

Kambun girma na ayukansu,

Mawakan baka sun bi su,

Kai Ala da Naziru sun sansu,

Ai daraktotin kanywood sun bisu,

Malamman Zaure da islamiya sun amincesu.

Malam barkar mu da zuwan Babban da Sidi barkarmu, Mai gida Sama,Ila "tafiya mabudin ilmi" Ya ya Anty ta da sauran iyaye da yan uwa da abokan arziki?


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124