Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M77
=====Duniya Rawar yan mata=== KUSHUHA TA

BARI MUJI DR. A.A.JEGGA:

Ya ilahi mai niya,

Ga ni na zo na tsaya,

Gunka Neman lafiya,

Rabbi don wahadaniya,

Kar ka bari insha wuya,

In kiyama ta tsaya.

Ga ni dai wawa na ke,

Babu bauta na sake,

Na Riga na shantake,

Wajibi kuma in fake gunka sarki mai niya.

Yan uwa ga shawara,

In muna son gafara,

Said mu rudu da lahira karmu da mu da duniya.

A gaskiya muta ne ya kama ta mu sa ido mu kalli yan baitotin wannan waka. Kamar yadda Malam Sambo Wali Sakkwato ya CE.

"Kyawon magana in an yi ta,

Hankalin jama,a ya karkata ga Dubin manufatata....."

Ni na yarda kyan magana da anyi ta kowa ya mada hankali akanta. Don Son cin moriyarta.ko gane abin nufinta. Wani abin fahimta shi ko Malam na Bauchin Yakubu cewa ya yi.

"In za ka fada fadi gaskiya,

Ko mai ta ka jamaka ka biya....."

Kuma haka abin ya ke, in ka fadi gaskiya,da wuya mutane ba su nuna ma tsamgwama ba. Sai dai kalilan daga mutanen.

To shi ko Baban Amina,mai rigar waka(Ala) cewa ya yi.

"...Dan uwa fa harshenka,

Zakinka da zaya cinyeka,

In ka iya bakinka,

katsirar da rayuwa taka....."

Jama,a mu na cikin mashi,a mu kula da al,kalaminmu. Mu kula da tunaninmu, mu kula da harshenmu,mu yi ma kan mu kiya mu laili.

KUSHUHA TA

Ni lamari na ka sani Marsala da hakken da ya rataya akai na, kuma INA ganin yawan rauni na. Da yawan matsaloli na a rayuwa. Ni dai gani sai tunanin hakken Allah da iyaye da sauran mutane. Amma gani da mugu-mugun rauni. Ga laifi ya yi min yawa. Allah ka kubutar da ni. Ka kubutar da iyaye na,ka kubutar da malammai na,da masu gida Jena,da dukkan musulmi. Ga shairin shaidan makiyinmu,YAA ALLAH!YAA ALLAH!!


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124